Palasdinawa Sunki Amincewa da Sabbin Dokoki Kan Masallacin Kudus

Mahukuntan da suke lura da al’amurran masallacin Kudus sun yi fatali da sabbin dokoki da ka’idoji da mahukuntan Isra’ila suka shimfida bayan faruwar musayar wuta wadda ta janyo rasa rayuka kwanakin baya har aka kulle Masallacin.

Hukumomin addinin musulunci wadanda ke sa ido da gudanarwa a masallacin, sun ki amincewa a yi sallah a ranar Lahadi bayan da mahukuntan Isra’ila suka kafa sabbin na’urorin tsaro da masu daukar hotuna a ko’ina.

“Rufewa tare da mamaye harabar masallacin Kudus, da kuma hana kiran sallah ba adalci ba ne, kuma abu ne wanda ya saba da dokokin Majalisar Dunkin duniya tare da yarjejeniya ta kasa da kasa”, a cewar Omar Kiswani, wani babban darakta na masallacin Kudus din yayin da yake zantawa da manema labarai.

“Ba za mu taba amincewa da wadannan sauye-sauye da Isra’ila ta kawo a Masallacin Kudus ba, wannan kokarinta na karbe gudanarwarsa daga garemu. Za mu kasance a wajen masallacin har sai an mayar mana da abun da aka karbe mana”.

Isra’ila ta rufe Masallacin Bayan musayar wuta da ta faru tsakanin wasu matasan Palastinawa da ‘Yan sanda. Daruruwan masallanta ne suka taru a kofar shiga farfajiyar masallacin, kusa da mashigar Kofar ‘Lion’ wadda ke tsohon birni akan idon jami’an tsaron Isra’ila.

Wannan shine karo na farko da aka rufe farfajiyar Masallacin ga masu yin sallah a cikin shekaru 48.

 

 

1711total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.