A siyasan ce za a magance matsalar Venezuela

Shugaban kasar Argentina Mauricio Macri ya sheidawa mataimakin shugaban Amurka Mike Pence cewar basa goyan bayan kai hari Venezuela domin magance rikicin siyasar kasar.

Mauricio Macri ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da Pence wanda ke ziyarar wasu kasashen dake yankin, shugaba Macri yace ta hanyar siyasa ne kawai za’a magance rikicin na Venezuela.

Argentina itace kasa ta baya bayan nan da ta fito karara ta bayyana adawar ta da yunkurin na shugaba Donald Trump na daukar matakin soji kan Venezuela.

Asalin Labari:

RFI Hausa

396total visits,1visits today


Karanta:  Amurka ta saka wa jami'an Venezuela 13 takunkumi

Leave a Reply

Your email address will not be published.