Adamawa: Tashin Hankali Tsakanin Fulani Makiyaya Da ‘Yan Yankin Kwateh

Rahotanni daga jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya na cewa kimanin rayuka hudu ne aka rasa a wani sabon rikici dake neman barkewa a tsakanin Fulani Makiyaya da kabilun yankin Kwateh a yankin karamar hukumar Girei.

An tabbatar da cewa rikicin na neman tashi ne biyo bayan kashe wasu Fulani makiyaya biyu, inda suma fulanin suka kashe wasu mutanen yankin biyu a wani harin daukar fansa.

To sai dai tuni wannan lamarin yakai ga fara kona gidajen wasu Fulani makiyaya a yankin, kamar yadda shugaban karamar hukumar Girein Alhaji Hussaini Masta, ya tabbatar ta wayar talho.

To sai dai kuma, rundunar yan sandan jihar Adamawan, ta bakin kakakinta SP Othman Abubakar, ta danganta lamarin da cewa yan fashi da makami ne sukayi kisan.

A baya dai yankin yayi fama da tashe tashen hankula dake da nasaba da fadan kabilanci a tsakanin al’umomin biyu, lamarin da ya jawo asarar rayuka da dukiya, batun da ya kai kafa kwamitocin sasantawa, wanda kawo yanzu da alamun basu fara haifar da mai ido ba.

Asalin Labari:

VOA Hausa

6463total visits,2visits today


Karanta:  Kotu Ta Bayar Da Umarnin Kai 'Yan IPOB 67 Kurkuku

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.