Ahmad Musa Ya Kusa Komawa Kulab Din Hull City Da Taka Leda

Saura kiris kulub din Hull City ya yarda da yarjejeniyar da zata baiwa dan wasan gaba na Leicester City Ahmed Musa sake saduwa da Leonid Slutsky a Sitadiyon din KCOM.

Tuni zance yayi nisa tsakanin kulublikan guda biyu ana kuma kyautata zaton yarjejeniyar zata bayar da damar bada dan wasan mai bugawa Nijeria wasa aro na tsahon kaka guda kafin rufe siyan ‘yan wasa a yau din nan.

Bada aron Ahmed Musa wata dama ce mai kyau ga kulub din na City watanni 14 kacal da Leicester ta siyo shi kan farashin da yakai £17m

Dan wasan mai shekaru 24 yayi kokarin nuna kansa a Gasar Firimiya sai dai damar sake aiki tare da  Slutsky bayan nasarorin da suka samu tare a kulub din CSKA Moscow na neman kubuce masa.

Neman Ahmed Musan kokari ne cikin kokari uku da City keyi kafin rufe cinikayyar ‘yan kwallon.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

274total visits,1visits today


Karanta:  Bertrand Traore ya koma Lyon a kan fam 8.8m

Leave a Reply

Your email address will not be published.