Ahmed Makarfi Yayi Hadarin Mota

Shugaban rikon kwarya na Jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP, Sanata Ahmed Makarfi ya tsallake wani hadarin mota a jiya (29 July 2017) a hanyar sa ta zuwa jihar Kaduna daga babban birnin tarayya Abuja.

Wata majiya ta bayyana cewa motar Sanata Makarfi tayi karo da wata mota a kan babban titin na Abuja zuwa Kaduna.

A wata sanarwa da Kakakin Jam’iyyar Prince Dayo Adeyeye ya fitar ya bayyana cewar shugaban na rikon kwarya bai jikata ba ko kadan. Haka zalika babu wani wanda yaji ciwo a cikin motar tasa.

Sai dai har izuwa lokaci wallafa labarai babu wani bayani game da daya motar da suka yi karo a kan hanyar.

2087total visits,1visits today


Karanta:  Ba zan nemi gafarar Buhari ba – Buba Galadima

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.