Aisha Buhari ta sake komawa London mijinta

Uwargidan Shugaban Najeriya Hajiya Aisha Buhari ta sake tafiya Birtaniya domin duba lafiyar mijinta Muhammadu Buhari wanda ya shafe makonni da dama yana jinya a can.

Wata sanarwa da mai magana da yawunta, Suleiman Haruna, ya fitar ta ce: “za ta isar wa shugaban sakonnin alheri da al’ummar kasar ke aika masa”.

Ya kara da cewa a safiyar ranar Litinin ne Hajiya Aisha ta bar Najeriya amma sai Talata za ta isa London saboda za ta yada zango a kasar Habasha domin halartar taron matan shugabannin kasashen Afirka kan cutar kanjamau.

Kusan wata biyu kenan da Shugaba Buhari, mai shekara 74, ya bar kasar zuwa Birtaniya – wadda ita ce tafiyarsa jinya karo na biyu a bana.

A watan da ya gabata ma ta ziyarci mijin nata inda bayan ta dawo ta shaida wa manema labarai cewa yana samun sauki sosai kuma ya kusa koma wa gida.

Tun bayan tafiyarsa, sau daya tak aka ji amonsa, lokacin da ya aike da sakon sallah ga al’ummar Musulmin kasar.

Rashin lafiyar shugaban tana ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce sosai a kasar, inda wasu ke ganin kamata ya yi shugaban ya yi murabus don fuskantar kula da lafiyarsa.

Amma wasu kuwa suna ganin tun da ya mika ragamar shugabanci a hannun mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, to babu wani abin damuwa.

Har yanzu dai ba a san takamaimai cutar da ke damun Shugaba Buhari ba.

  • 19 ga watan Janairu ya tafi Birtania hutun jinya
  • 5 ga watan Fabreru ya nemi majilisa da ta tsawaita hutun nasa
  • 10 ga watan Maris ya dawo gida to sai dai bai koma aiki ba kai tsaya
  • 26 ga watan Afrilu ya kasa halartar taron majalasar zartarwa karo na biyu, inda ya rinka “aiki daga gida”
  • 28 ga watan Afurilu bai halarci Sallar Juma’a ba
  • 3 ga watan Mayu bai halarci taron majalisar zartarwa ba karo na uku jere
  • 5 ga watan Mayu ya halarci Sallar Juma’a a Abuja
  • 6 ga watan Mayu ya sake tafiya Birtaniya neman magani
  • 6 ga watan Yuni Aisha Buhari ta ce yana samun sauki sosai
Karanta:  Abinda ‘Yan Najeriya Ke So Buhari Ya Fara Tunkara

449total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.