Al-Shabaab ta kama wani yanki mai arzikin uranium a Somalia

Gwamnatin Somalia ta bukaci taimakon gaggawa daga Amurka na ta hana mayakan kungiyar al-Shabaab samar da makamashin Uranium da ake hada makamin kare dangi da shi, ga kasar Iran.

A wata wasika da ministan harkokin kasashen waje na Somalia, Yusuf Garaad ya aika wa Washington, ya ce al-Shabaab ta kama wani yanki da ke da tarin sinadarin na Uranium kuma tuni ta fara aikin hako shi.

A wani bincike da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta taba yi, ta ce Somalia na da arzikin uranium a jibge, amma ba a fara inganta shi ba.

Wannan ikirarin da za a iya cewa kusan na daban wanda gwamnatin Somalia ta yi dai, abu ne da ba wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da shi nan take.

Sannan kuma hukumomin na Somalia ba su bayyana a fili yadda ‘yan kungiyar fafutukar, masu ikirarin Jihadi ke aikin hakar makamashin na uranium ba.

Sannan ba kuma wata sheda da suka gabatar da ta tabbatar da cewa ‘yan al-Shabab din na aiki a kai ko kuma shirinsu na aika wa Iran sinadarin na hada makamin nukiliya.

Wasikar ta kuma bayyana cewa al-Shabaab tana da alaka da kungiyar IS, wanda a bayyane take tun da dadewa cewa tana da dangantaka da al-Qaeda.

Mogadishu dai na wannan kira ne na gaggawa ga Amurka, na neman dauki, da cewa wannan matsala ta yanzu ta fi karfin hatta dakarun kungiyar kasashen Afirka ta AU da ke Somaliar.

Kawo yanzu ma’aikatar harkokin kasashen waje ta Amurka ba ta bai wa gwamnatin Somalia amsar wasikar ba, amma kafofin watsa labarai na Amurka sun tabbatar da cewa Washington ta samu wasikar.

Masu fashin baki dai na ganin Somalia ta yi wasikar ne da nufin samun tarin sojojin Amurka a kasar, inda al-Shabaab ke kai munanan hare-hare.

Karanta:  Turai: Macron Na Jagorantar Taron Magance Kwararar Bakin Haure
Asalin Labari:

BBC Hausa

634total visits,3visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.