Albashir: ICC ta ce Afrika ta Kudu ta keta doka kan kin kama Albashir

Kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya, ta yanke hukuncin cewa gwamnatin Afrika ta Kudu ta keta doka da ta ki kama shugaban Sudan duk da cewa kotun ta bayar da umarnin a kama shi.

Hakan na zuwa ne, shekara uku bayan hukumomin Afrika ta Kudu sun bar shugaba Omar Al Bashir ya bar ƙasar lokacin da ya je halartar wani taron koli na kungiyar tarayyar Afrika.

Ana tuhumarsa da laifin kisan kiyashi a Darfur, amma tsawon shekaru ke nan , da shugaba Omar Al Bashir ke tafiye-tafiye a Afirka, yana ziyartar shugabannin da ke da ra’ayin kotun hukunta manyan laifukan yaki, ba ta adalci ga nahiyar.

A ranar Alhamis ne, kotun ta mayar da martanin cewa gwamnatin Afrika ta Kudu, ta gaza a aikinta, da ta yarda Shugaba Al Bashir ya bar ƙasar bayan wani taron kungiyar Afrikar a shekarar 2015.

Kotun ta bayyana abin da ke bayyane ne, sai dai mutane sun sa ran lauyoyin Afirka ta Kudu za su iya ba da hujja da doka, amma basu iya yin hakan ba.

Afrika ta Kudu dai, mamba ce a Kotun hukunta manyan laifukan yaki kuma ta san dokokin.

A baya nahiyar na goyan bayan ICC, amma yanzu Afirka ta Kudu da wasu ƙasashe da dama na samun sauyin ra’ayi, inda suke ganin kotun ba ta yi wa Afrika adalci.

Saboda hakan suna ganin cewa kafa cibiyoyi masu zaman kansu a nahiyar shi ne mafita a nan gaba.

ICC dai ta tsaya a kan bakan ta, kuma za ta iya kai karar Afirka ta Kudu ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, amma kawo yanzu ba ta dauki wannan matakin ba.

Karanta:  Amurka za ta sayar wa Nigeria jiragen yaki
Asalin Labari:

BBC Hausa

755total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.