Tarihin Alhassan Doguwa

Alhassan Doguwa

Alhassan Ado Garba wanda aka fi sani da “Alhassan Ado Doguwa” wani dan siyasa ne a jihar Kano dage Najeriya. An haifi Alhassan Doguwa a ranar sha hudu ga watan Augusta na alif dari tara da sittin da biyar (Saturday, 14 August 2965) a garin Dadin Kowa dake karamar hukumar Doguwa a jihar Kano, Najeriya.

Alhassan Doguwa ya kasance bulaliyar majalisar tarayya a jamhuriyya ta hudu, karni na biyar. Ya kasance a majalisar wakilai tun a shekara ta dubu biyu da bakwai (2007) wanda ya fara cin zaben sa a karkashin jam’iyyar PDP mai mulki a wancan lokacin.

Alhassan Doguwa ya taba zama zababben dan majalisar wakilai a jamhuriyya ta uku, karni na daya a shekara ta alif dari tara da casa’in da biyu (1992) a karkashin jam’iyyar SDP.

Kuruciya da Ilimi
An haifi Alhassan Doguwa a ranar Asabar sha hudu ga watan Augusta na alif dari tara da sittin da biyar (Saturday, 14 August 2965) a garin Dadin Kowa dake karamar hukumar Doguwa a jihar Kano a Najeriya. Mahaifin Doguwa mai suna Alhaji Ado ya kasance shaharareen dan siyasa a karkashin jam’iyyar NEPU wacce take fitacciyar jam’iyya a shiyar Kano dake arewacin Najeriya wacce daga baya ta hade da jam’iyyar UPGA inda ta zama babbar jam’iyyar hadaka mai adawa da babbar jam’iyyar kasa. Mahaifin Doguwa ya kasance zababben dan majalisar dokoki ta jihar Kano a karkashin jam’iyyar PRP.

Alhassan Doguwa mai rike da kambun digiri mai lamba ta daya (First Class) a fannin jarida daga Jami’ar Bayero dake jihar Kano a Najeriya. Ya samu shiga siyasa a yayin da ya gama bautar kasa inda kuma aka zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai ta kasa a karkashin rushashiyar jam’iyyar SDP.

Siyasa
Kasancewar Doguwa a matsayin zababben dan majalisar wakilai ta kasa a karkashin rushashiyar jam’iyyar SDP a shekara ta alif dari tara da casa’in da biyu (1992) ya share masa fagen shiga siyasar Nijeriya. Doguwa ya kasance mutum haziki a yayin zaman sa a majalisar inda ya taimaka wajen tabbatar da Mohammed Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin mataimakin shugaban majalisar wakilai ta kasa.

A shekara ta dubu biyu (2000) Doguwa ya samu nadin mai bawa gwamna shawara a harkar muhalli a karkashin tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso. Sannan ya kasance mai bada shawara na musamman ga shugaban majalisar Dattijai ta kasa Cif Adolphus Wabara da kuma Kenneth Nnamani a tsakanin shekara ta dubu biyu da uku (2003) zuwa shekara ta dubu biyu da shida (2006).

A shekara ta dubu biyu da bakwai (2007) Doguwa ya kasance zababben dan majalisar wakilai ta kasa a karkashin jam’iyyar PDP inda kuma ya rike mukamin mataimakin shugaban kwamiti mai kula da yankin Neja Delta. Ya sake samun nasarar cin zabe a shekara ta dubu biyu da sha daya (2011) duka dai a cikin jam’iyyar PDP inda wannan karon ya rike mukamin shugaban kwamitin cigaban karni (MGDs).

A shekara ta dubu biyu da sha hudu Doguwa ya samu komawa jam’iyyar adawa ta APC tare da sauran ‘yan majalisun jihar Kano a karkashin jagorancin gwamna Rabiu Kwankwaso inda kuma ya samu lashe zabe a shekara ta dubu biyu da sha biyar (2015)

Alhassan Doguwa ya kasance bulaliyar majalisar wakilai ta kasa inda kakakin majalisar Yakubu Dogara ya tsaya kai da fata wajen ganin an tabbatar dashi a wannan kujera inda amincewar sa ta kawo babbar takaddama a majalisar ta kasa.

Sarauta
Doguwa ya samu nadin sarautar gargajiya ta Sarkin Yakin Burum Burum da kuma Yariman Dadin Kowa wanda hakimin Doguwa da kuma na Tudun Wada suka nada shi a shekarar dubu biyu da uku (2003).

Doguwa ya sake samun nadin sarautar Dallatun Kangiwa by sarkin Kabbin Jega.

Shafukan Sada Zumunta
Website: http://www.nass.gov.ng/mp/profile/781
Twitter: Alhassan Doguwa
Facebook: Alhassan Doguwa
Wikipedia: Alhassan Doguwa

1687total visits,1visits today