Ali Nuhu ya ƙaddamar da fim ɗin Mansoor

Fim ɗin Mansoor, wanda fitaccen jarumin Kannywood Ali Nuhu ya shirya kuma ya ba da umarni, labari ne na wani matashi ɗan gaba da fatiha.

Mahaifiyar Mansur ta yi ƙoƙarin ɓoye masa wannan sirri game da asalinsa, sai dai soyayya ta sanya shi neman sanin gaskiyar al’amari.

Iyayen wata yarinyar da soyayya ta hada su a sakandare ne suka yi masa gorin asali, inda hakan ya tilasta masa katse karatu, ya bazama duniya don gano mahaifinsa.

An ƙaddamar da fim ɗin Mansoor ranar Alhamis ta hanyar nunin farko, a wani gawurtaccen biki cikin wata silima da ke birnin Kano, kuma sai a nan gaba ne za a fitar da faya-fayensa na bidiyo.

Sama da shekara goma da fara tunanin wannan fim, wanda aka shafe fiye da shekara biyu ana tsarawa da haɗa shi.

Daraktan fim ɗin, Ali Nuhu ya ce jigon Mansoor shi ne juriya da tawakkali don samun waraka ga wani halin alhini da ɗan’adam ka iya fuskanta a rayuwa.

“Akwai soyayya a cikinsa, amma jigonsa ba soyayya ba ce. Darasin da yake ƙoƙarin isar wa al’umma shi ne duk abin da ka ga ya samu mutum a rayuwa…kar ka yi masa gori.

Kar ka tsangwame shi a kan wannan abu. Domin mai yiwuwa hanyar da Allah ya jarabce shi kenan, kamar yadda kai ma a matsayinka na ɗan’adam akwai hanyar da Allah ya jarabce ka.”

Saɓanin yadda aka saba ganin fitattun jarumai a fina-finan Kannywood, a wannan karon an yi amfani da wasu sabbin fuskoki a matsayin manyan jarumai, da suka haɗar da Umar M Sharif da Maryam Yahaya.

Sama da shekara 20 kenan da fara harkar fina-finan Kannywood, amma masu sharhi na sukar cewa ba a sanya fasahar zamani sosai a cikin fina-fianan.

Karanta:  An Gudanar da Jana'izar Kasimu Yero a Kaduna

Sai dai masu fim ɗin Mansoor sun ce sun yi ƙoƙarin tunkarar wannan ƙalubale wajen haɗa shi, don haka ne ma a cewarsu, fim ɗin ya kasance mafi tsada a duniyar Kannywood, don kuwa an kashe kusan naira miliyan takwas wajen hadawa da tallata shi.

2928total visits,3visits today


2 Responses to "Ali Nuhu ya ƙaddamar da fim ɗin Mansoor"

  1. Mohd young minister   July 1, 2017 at 2:38 pm

    That’s why I love working with FKD TEAMS ALI NUHU always comes with new ways of keeping Kannywood ALIVE

    Reply
  2. PC ISMAIL YA'U YA'U   July 3, 2017 at 12:11 pm

    Up-up FKD, I LOVE YOU SO MUCH

    Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.