Almajiranci: Kungiyar NEEM ta yunkuro don kawo karshen cin zarafin alamjirai

Daga Zainab Sani

An bayyana cewa yin gyara da kawo canji a harka almajiranci abu ne da yake bukatar gudummawar dukkanin al’umma. Shugaban Kungiyar NEEM FOUNDATION kungiyar da ke fafutukatun kawo karshen cin zarfi tare da bautar da almajirai a fadin kasar nan Ashraf Usman ne ya bayyana haka a wani taron tattauna da kungiyar ta yi tsakaninta da ‘yan jaridun da ke Jihar Kano.

A cewarsa harkar almajirci babban qalubale ne da yake buqatar haxin kan kowa da kowa tun daga kan iayyen almajiran da malamansu da gwamnati da al’ummar gari. “wanann ba abu ne na wani vangare xaya ba, yaqi ne da yake buqatar gudummawa dgaa kowane vangare domin a fitar da jaki daga duma. Iyayen almajiran suna da rawar takawa, wajen sauke nauyin da Allah ya dora musu na kula da yayan da suka haifa. Haka su ma  alarammomi akwai bukatar su sanya idanu akan almajiran da ake kawo msuu na kula da karatunsu da kuma lafiyarsu. Ita a,m gwamnati a nata bangaren nauyi ne akan ta babab na kula da almajiran nan kasancewar su ma yan kasa ne kamar sauran ‘ya’yan jama’a”

Tunda farko a jawabinsa Asharf Usman ya bayyana cewa  qungiyar ta fito da shiri mai taken ‘Be the voice: Reforming Almajiranci” ne don lalubo hanyar da za a kawo karshen cin zarafi da alamjirai ke fuskanta ta fuskoki daban-daban a fadin Jihar Kano. “Mun fuskanci cewa almajirai na fuskantar cin zarafi ta fuskar bautarwa da sanya su tafarkin aikata miyagun laifuka, baya ga tsintar kansu da suke yi a hannun ‘ya’yan kungiyoyin asiri, don haka muka fito da wanann shiri don ganin an tsaftace tare da kyautata harkar almajiranci gaba daya”

Har ila yau Kungiyar ta Neem Foundation ta nemi hadin kai da kafafen watsa labarai da ke fadin Jihar Kano don ganin an magance matsalar cin zarafin da ake yi wa almajirai a fadin kasar nan.

Karanta:  Kungiya Ta Dauki Nauyin Almajarai 300 Karatun Boko

Da suke mayar da jawabi ‘yan jaridun wadanda suka fito daga kafafen watsa labarai daban-daban sun bayar da tabbacin bayar da goyon baya ta hanyar wayar wa al’umma kai don fahimtar illar da ke cikin cin zarafi da bautar da almajirai tare da yin kira gare su don su bayar da tasu gudummawar wajen gyara tare da canza tsarin harkar almajirci gaba xaya.

900total visits,3visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.