Ambaliyar ruwa ta tsayar da al’amura a Lagos

Al'amura sun tsaya cak, yayin da mutane suka kasance a gida a wasu sassan birnin Legas da ke kudancin Najeriya, bayan wani ruwansa da aka kwashe kwanaki ana yi ya haddasa ambaliyar ruwa.

Mazauna unguwannin Lekki da Victoria Island sun wari gari ranar Asabar da ambaliyar ruwa bayan kwashe kwana biyar a ruwa, kamar yadda wata wadda take zaune a Legas ta shaida wa BBC.

“Yau kwana biyar ke nan ana ruwa babu dauke wa a unguwar Lekki. Ko ‘ya’yanmu ma a cikin ruwa suke zuwa makaranta cikinsa suke dawowa,” in ji ta.

Har ila yau, wata ganau ta shaidawa BBC cewa: “Ruwa marka-marka ake yi a nan Legas wanda kuma hakan ya sa mu da yaranmu mun kamu da mura.”

Kodayake babu rahotan da ke cewa an samu asarar rai, amma mazauna yankin da abin ya faru sun ce sun tafka mummunar asara.

Ruwan ya rika shiga cikin gidajen jama’a yayin da a wasu unguwannin ambaliyar ta tilasta wa jama’a fara amfani da kwale-kwale don yin zirga-zirga.

Hakazalika, ambaliyar ta jawo dauke wutar lantarki a wani bangare na birnin saboda yadda falwayoyin wutar lantarki suka fadi.

Ana danganta rashin samar da hanyoyin ruwa yadda ya kamata da babban dalilin da yake jawo ambaliyar ruwa a birnin.

Asalin Labari:

BBC Hausa

775total visits,1visits today


Karanta:  Mutane 15 ne ambaliyar ruwa ta kashe a Suleja

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.