Amurka Ta Saidawa Najeriya Jiragen Yaki 12

Ma’aikatar tsaron Amurka ta shaidawa Majalisar kasar saidawa Najeriya jiragen sama na yaki 12, da kuma sauran makaman da kudin su ya kai Dala miliyan 593, domin amfani da su wajen yaki da kungiyar Boko Haram.

Ofishin hadin kan tsaro na Amurka, yace cinikin ya kunshi tarin bama bamai da makaman roka wanda tsohuwar gwamnatin shugaba Barack Obama ta amince da shi.

Ana sayar da kowanne jirgin yaki kirar Super Tucano A-29 wanda ake kai hari da shi da kuma ayyukan leken asiri, akan dala miliyan 10, kuma kamfanin Embraer na Brazil ke kera shi.

A baya, an jinkirta cinikin ne, sakamakon harin kuskure da sojin Najeriya suka kai kan ‘yan gudun hijira a Borno, wanda ya hallaka mutane akalla 170, amma daga bisani, gwamnatin Donald Trump ta amince a mikawa Najeriya jiragen.

Asalin Labari:

RFI Hausa

412total visits,1visits today

Karanta:  'Malamai 70 sun bar jami'ar Maiduguri saboda Boko Haram'

Leave a Reply

Your email address will not be published.