An cafke mutane 24 da ake zargi ‘Yan Boko Haram ne a Jihar Edo

Rundunar Sojan Najeriya ta bada sanarwar cafke wasu mutane ashirin da hudu wadanda ake zargin ‘yan kungiyar tada kayar baya ne, ta Boko Haram.

Babban kwamandan Makarantar Horar da aikin Injiniya ta Sojan Najeriya dake garin Auchi a Jihar Edo ne ya sanar da hakan lokacin da ya ziyarci fadar basaraken Gargajiya na Masarautar Auchi, Mai Girma Alhaji Aliru H. Momoh.

Kwamandan yace an cake wadanda ake zargin ne a yankin masarautarsa, kuma tuni aka tusa keyarsu zuwa garin Benin domin ci gaba da bincike. Ya kuma kara da cewar wadanda ake zargin suna yin shofar burtu ne tare da fakewa da fulanin dake zaune a yankin domin gudanar da aiyukansu.

A nasa bangaren Basaraken Gargajiyan Mai girma Alhaji Aliru H. Momoh, ya yabawa jami’an rundunar Sojan tare da kira ga jama’a da su ci gaba da sanya idanu tare da bawa jami’an tsaro goyon baya.

995total visits,4visits today


Karanta:  'Yan Boko Haram 240 sun mika wuya bayan farmakin soji

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.