An Daure Wani Ma’aikacin Gwamnati Saboda Zagin Gwamna Dankwambo

Wata Kotun Majistire a Gombe ta tsare wani ma’aikacin gwamnatin jihar a kurkuku saboda zarginsa da zagin Gwamnan Jihar Ibrahim Hassan Dankwambo da mahaifiyarsa.

Inuwa Dattijo wanda akafi sani da suna Maitaya wanda ke aiki da hukumar walwala ta jihar ne ya shigar da Abubakar Adamu dan shekara 35 wanda ke aiki da ma’aikatar ilimi ta jihar kara bisa zargin cewa wanda ake zargin ya aika masa da fefe mai dauke da zagin gwamnan da mahaifiyarsa.

Kamar yadda Rahotan Farko na ‘Yansanda (FIR) ya nuna da ake karantawa wanda ake zargin a kotu, ranar 9 ga watan Satumba Adamu ya tura da fefen mai dauke da zagin wayar DJ Maitaya yana mai cewa ya same shi ne daga gurin wani wanda bai san kowanene ba.

Dan sanda mai shigar da kara Sifeto Habibu Danjuma ya fadawa kotu cewa lokacin da aka tambayi wanda ake zargin daya bayyana wanda ya turo masa sakon, ya gaza bada tartibin bayani mai gamsarwa.

An tuhumi wanda ake zargin da laifi guda na bada shaidar kanzan kurege. Laifin da ya saba da sashi na 156 na kundin laifuffukan jihar, a cewar Sifeto Danjuma. Wanda ake zargin ya musanta zargin da ake yi masa.

Dangane da korafin nasa kuwa, Alkalin Kotun Majistirin Japhet Maida ya ummarci a sakaya wanda ake zargin a gidan yari.

Ya kuma daga shari’a zuwa 26 ga watan Satumba kamar yadda mai gabatar da kara ya nema.


2478total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.