An daure ‘yan makaranta kan wasa da Boko Haram

Wata sanarwar da Kungiyar Amnesty International ta fitar ta ce Jami'an tsaro sama da goma sun rufe dakin taron da ke wani otal a Yaunde, babban birnin Kamaru domin hana taron manema labarai da zai yi kira a saki 'yan makarantar da aka daure kan laifin rashin "yin tir da ayyukan ta'addanci."

An kama yaran ne bayan an samu wanin sakon tes a wayoyinsu na salula game da kungiyar masu tada kayar baya ta Boko Haram.

Sakon tes din da aka samu wayoyin ‘yan makarantar dai yana raha ne kan Boko Haram da kuma wuyar samun aiki a Kamaru.

“Boko Haram na daukar mutanen da suka dara shekara 14 aiki. Sharadin daukar shi ne: Kiredit hudu a jarabawar GCE ciki har da addini,” in ji sakon tes din.

Da wani malami ya gane sakon tes din, sai ya kwace wayar kuma ya sanar da ‘yan sanda. An kama matasan uku, kuma aka daure su a watan Janairun shekarar 2015, inda aka daure su da sarka, in ji sanarwar kungiyar Amnesty International.

A watan Nuwamban bara ne dai aka samu matsan da laifin rashin yin tir da ayyukan ta’addanci kuma aka yi musu daurin shekra goma-goma.

Daliban da suka hada da Fomusoh Ivo Feh da Afuh Nivelle Nfor da kuma Azah Levis Gob daukaka kara bisa samun da laifin kuma a ranar 15 ga watan Yuni ne dai za kotu za ta saurari daukaka karansu.

Ita gwamantin kasar ta tabbatar da hana taron manema labaran bisa barazanar da ta ce taron take wa doka da oda.

Ministan Sadarwar kasar, Issa Tchiroma, ya tabbata ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters ta wayar tarho cewar idan zanga-zanga tana barazana ga doka da oda, hukumomi na ikon hana ta, kuma abun da aka yi kenan kan taron Amnesty International.

Ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula na sisaya a Kamaru tun watanni bakwai da suka wuce bisa mulkin shugaba Paul Biya mai tsawo inda ake matsawa shugaban lamba gabanin zaben shekarar 2018.

Karanta:  Halin da muka samu Shugaba Buhari a ciki — Rochas Okorocha

Kasar Kamaru dai tana cikin dakarun kawancen da ke yaki da kungiyar Boko Haram wadda ta kashe sama da mutane 20,000 inda ta raba miliyoyin mutane da gidajensu.

Asalin Labari:

BBC Hausa

388total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.