An fara rububin bargo a kasuwa

Yayin da sanyin hunturu ke dada kankama, kasuwar bargo ta fara samun tagomashi, bayan tsawon wani lokaci da masu sayar da shi suka yi fama da rashin masaya, in ji wani dan kasuwa a Najeriya.

Usaini Sa’idu Zakirai, mai sayar da bargo a Kaduna ya ce alhamdulillahi! Yanzu kasuwa ta fara garawa don kuwa ana bukatar bargo.

Ya ce suna sayar da baguna kama daga na kimanin naira 1,500 har zuwa na naira 7000, sakamakon shigowar sanyi.

Sai dai a wasu lokuta idan sanyi ya yi tsanani, bargon yakan rage dumi, abin da ya sa wasu mutanen kan yi amfani da wuta don gasa jiki da samun wartsakewa.

Abin wani mazaunin Kaduna, Malam Abdulwahab ka cewa na da matukar hatsari ko da yake, kusantar wutar na da dadi ga jiki lokacin sanyi amma ta fi saurin haddasa gobara.

“Akwai mutanen karkara har ma da na maraya da sukan sa wuta a wurare da yawa, kuma tana iya kwacewa ta je ta cutar da mutum shi kansa da ma na kusa da shi,” a cewarsa. Don haka sai an yi hattara.

Shi ma wani magidanci Lawan Sani ya ce shigowar sanyin bana ke da wuya, ya yi kokarin yi wa ‘ya’yansa tanadi don gudun yi musu lahani.

Asalin Labari:

BBC Hausa

32203total visits,1visits today


Karanta:  An kama wani mawaki kan yin rawar dab a Saudiyya

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.