An gano daliban ‘boge’ 706 a Sokoto

Gwamnatin Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta gano daliban boge 706 da suka yi yunkurin samun tallafin karatu daga asusun jihar.

Wani kwamiti da gwamnatin jihar ta kafa domin yin bincike kan hakikanin adadin daliban da suka cancanta a bai wa tallafin karatu ne ya gano hakan.

Kwamitin, wanda Ambassador Shehu Wurno ya jagoranta, ya ce hakan ya sa jihar ta tara naira miliyan 29.

Ambassador Wurno ya shaida wa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, a lokacin da yake mika masa rahoton bincikensu cewa, kwamitin ya ziyarci makarantun gaba da sakandare 40, a ciki da wajen Najeriya kuma sun tantance daliban jihar 14, 532 wadanda suka cancanci samun tallafin karatu.

“Mun tabbatar cewa kudin karatun daliban a shekarar karatu ta 2016/2017 sun kai N544, 613,724.00 yayin da alawus dinsu ya kai N143,560,855.00.

Haka kuma daliban na bin jihar N688,174,579.00 na yin rijista a makarantunsu a shekarar karatu ta 2016/2017,” in ji shugaban kwamitin.

Gwamnan jihar dai ya yaba wa mambobin kwamtin a kan aikin da suka yi, yana mai shan alwashin ci gaba da mayar da hankali wurin inganta ilimi.

Batun biyan tallafi ga daliban jihar dai ya jawo ce-ce-ku-ce sosai, saboda Sokoto, kamar wasu jihohin kasar, na da dalibai da dama da ta tura kasashen waje.

Asalin Labari:

BBC Hausa

579total visits,1visits today


Karanta:  Iyaye da dalibai sun koka kan yajin aikin ASUU

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.