An Gano Masu Kamfanin Da Suka Shigo Da Makamai

Sun Yiwa Kamfanin Su Rijista Da Adireshin Gidajen Zama

Mutanen uku mazauna Abuja da lagos sukeda mallakin kamfanin nan da ake dangantawa da shigo da makamai kasarnan ba bisa ka’ida ba a farkon makon nan, kamar yadda binciken kamfanin jaridar Daily trust ya nuna.

Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kasa wato Kwastam ranar Alhamis ta fidda sunan kamfanin Great James Oil and Gas Ltd a matsayin wanda ya shigo da bindigu 470 wadanda aka kama a tashar jirgin ruwan kasar ne dake Tin Can Island a Legas satin da ya wuce, sati daya tsakani, a wannan tashar jirgin ruwan, aka kara kama wasu kunshin makaman mai dauke da bindigu 1,100 mallakar wannan kamfanin dai.

Shugaban Hukumar ta Kwastam Kanal Hamid Ali Mai Ritaya yace anyi amfani da wannan kamfanin mai suna Great James Oil and Gas Ltd don daukar makamai zuwa kasa Nijeriya. Sai dai shugaban na Kwastam bai bayyana sunan masu wannan kamfanin ba.

Binciken da kamfanin jaridar Daily Trust ya gudanar ya bayyana cewa Ayogu Cyril, Ayogu Kelvin da Ayogu Great James su suka yiwa kamfanin man rijista a matsayin Daraktocin kamfanin ranar  20 ga watan Yuli shekarar 2011. Anyi rijistar kamfanin da namba RC 968675.

Daraktocin uku sunyi amfani da adireshin unguwar Kaura dake Babban Birnin Tarayya da kuma unguwar Bariga dake Legas domin yiwa kamfanonin nasu rijista.

Cyril da Great James sun bayar da adireshin gurin zama da ke rukunin gidaje na 4, layi na 4, unguwar da ake yiwa lakabi da Prince and Princess Estate a cikin unguwar ta Kaura a Abuja. Shi kuma Kelvin ya bayar da adireshin dake rukunin gidaje mai namba 25 kan titin Bariga.

Karanta:  Sojin Lebanon Sun Dakatar Da Kai Wa Mayakan IS Farmaki

Lokacin da ‘yan jaridar Daily trust suka ziyarci adreshin kamfanin dake Abuja jiya, mai gadin gidan ya sanar dasu cewa mazaunin gidan na cikin gidan da matarsa. Lokacin da jam’an kamfanin  suka bukaci mai gadin da yayi musu magana da mai gidan nasa sai yaki yana mai cewa mai gidan nasa baya tsammanin wani bako a wannan lokacin.

Ande ga mota a ajiye a gaban gidan.

Mai gadin da wani mazaunin gidan sun musanta sanin wata alakar wani kamfanin mai ko mamallakin kamfanin da wannan gidan. Daga baya mai gadin ya shiga cikin gidan inda ya dawo da sakon cewa mai gidan nasa shima bashida masaniya da wancan kamfanin.

Wasu mutane mazauna gurin da aka zanta dasu cewa sukayi basu da masaniyar mai mazaunin gidan ke aikatawa a matsayin sana’a, wasu kuma cewa sukayi basa tunanin mazaunin wannan gida nada wani kamfanin mai me suna Great James Oil and Gas Ltd. “Mamallakin gidan daga kudu masu gabashin kasar yake, amma kuma ba sunansa James Ayogu ko Cyril Ayogu ba haka kuma bakon abu ne a gurinmu kamfanin da kuke alakanta shi dashi,” a cewar wani mazaunin gurin.

A can gida mai namba 25 kan titin Baraga, Karamar Hukumar Baraga a Jihar Legas, wanda aka bayar da cewa gidan Kelvin ne, gida ne launin ruwan kasa, hawa daya mai rukunin dakuna uku

Binciken da Daily trust ta gudanar ranar Lahdi ya nuna cewa tsarin ginin gida don zama akayi shi kawai.

Dukkanin mazauna ginin basa nan sai mutum daya lokacin da dan jaridar Daily Trust ya ziyarci gidan jiya, ya tattauna da mutumin. Yayin tattaunawa da mutumin wanda yaki yarda ya bayyanaa sunasa, cewa yayi tabbas Kelvin ya taba zama a gidan amma tuni ya tashi daga gidan ya koma gidansa tun misalin shekaru biyu da suka shude. Yace bai san adreshin gidan da Kelvin ya koma ba yanzu.

Karanta:  Najeriya: Majalisa Ta Amince Da Dokar Fallasa Barayin Gwamnati

Ranar Alhamis, shugaban Hukumar Kwastam yace kamfanin yayi amfanin da kayayyakin ruba a bil din da akayi amfani dashi wajen shigo da makaman don yaudarar jami’ai kan ainihin makaman da ake dauke dasu.

Yace an sami makamai 470 bayan mai’aikatansu sun tsayar da akwatin kayan mai lamba CMAU189817/8  domin gudanar da bincike.

An dai shirya gudanar da taron tattaunawa ranar Jumma’a tsakanin jami’an gwamnatin Nijeriya dana Turkiyya don duba yawan shigo da makamai Nijeriya daga Turkiyya.

A jimlance an kama makamai da suka kai yawan 2,671 a lokaci daban-daban har sau hudu cikin watanni takwas din baya dukkaninsu daga Turkiyya a cewar Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kwastam.

Hamid Ali yace hukumarsa da sauran hukumomin tsaro na gudanar da binciken dalilan shigo da makamai masu tarin yawa haka kasar nan.

“Har yanzu bamu kai ga gano dalilan ba, wadannan makaman an shigo dasu ne domin sayarwa, ko kuwa an shigo dasu ne domin a bawa kungiyoyi masu tada kayar baya ko masu rajin kafa kasarsu ko kuma masu garkuwa da mutane?” a  cewarsa.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

649total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.