An Gurfanar da Maharan Barcelona Gaban Kotu

Daya daga cikin Maharan birnin Bercelona da aka gurfanar da su yau gaban kotun Madrid babban birnin kasar Spain ya shaidawa kotu cewa suna shirye-shiryen kaddamar da wani gawurtaccen hari a kasar nan gaba kadan.

Da safiyar yau ne dai aka gurfanar da mutanen hudu da a ke zargi da hannu a tagwayen hare-haren na Bercelona gaban kotun da ke Madrid babban birnin kasar don amsa tuhuma, baya da ‘yan sanda suka halaka guda cikinsu a jiya wato Younes Abouyaaqoub lokacin da yake kokarin tserewa daga garin.

Maharin wanda aka bayyana sunan sa da Mohamed Houli Chemlal mai shekaru 21 dan kasar Marocco da aka shigo dashi kotun nannade da bandeji a jikinsa ya amsawa kotu cewa yana da hannu a kaddamar da harin wanda ya halaka mutum 16 bayan jikkata sama da dari.

Sauran Maharan da aka gurfanar gaban kotun a yau sun hada da Driss Oukabir mai shekaru 20 da Mohamed Aallaa 27 sai kuma Salh El Karib mai shekaru 30 dukkaninsu ‘yan kasar Marocco.

Bayan kammala sauraron shari’ar a karon farko da aka dauki tsawon mintuna 70, ana yi a cewar jami’in labaran kotun, ya ragewa babban alkalin kotun Fernando Andreu ya hakikance irin hukuncin da za a yankewa mutum 4 ko kuma ayi musu rikon wucin gadi kafin kammala shari’ar da zata kai ga yanke musu hukuncin karshe.

Jami’in labaran kotun ya shaidawa kamfanin dillacin labaran faransa na AFP cewa wadanda ake zargin sun bayar da wasu bayanan sirri da za a ci gaba da bincike akansu.

Asalin Labari:

RFI Hausa

883total visits,2visits today


Karanta:  Jirgi mai saukar ungulu ya kai hari kan kotun kolin Venezuela

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.