An kaddamar da manhajar yi wa mata kishiya

An kaddamar da wata sabuwar manhaja a kasar Indonesia don masu sha’awar yi wa matansu kishiya ta hanyar intanet.

Manhajar mai suna AyoPoligami wadda ta janyo takkadama a kasar wadda ta fi kowacce yawan Musulmai a fadin duniya, na ba wa maza masu sha’awar kara aure neman wata mata, har ma su yi zance da wasu mazan da ke da irin wannan niyya.

Mutumin da ya kirkiro manhajar Lindu Pranayama ya kare wannan fasaha da cewa za ta biya dumbin bukatun da ke akwai.

“Muna ganin wani al’amari inda maza masu yawan gaske ke neman kara aure, amma idan suka je shafukan hada soyayya, ba sa ganin zabin yi wa matansu kishiya.”

Ya ce ba a yi musu tanadi don neman karin aure na biyu ko na uku ko ma na hudu.

Sai dai masu fafutukar tabbatar da daidaiton jinsi na ganin wannan manhaja a matsayin wadda ke tunzura auren mace fiye da daya da kuma musguna wa mata.

Wata mai rajin tabbatar da daidaiton jinsi, Zakia Tunisa ta ce abin takaici ne da firgitarwa karon farko da ta ji batun wannan manhaja.

A cewarta kafin ma a samar da manhajar kara aure da ma auren mace fiye da daya ya yawaita.

Ta ce manhajar na ingiza auren mata da dama don ya samu karbuwa a tsakanin al’umma, mai yiwuwa ma kuma ya tilasta wa mata su yarda da shi.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1234total visits,1visits today


Karanta:  Mata sun yi kira da a kauracewa shafin Twitter

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.