An kaddamar da sashin “Nigeria for Buhari 2019”

An kaddamar da sabon shafin yanar gizo-gizo na “Nigeria for Buhari Project 2019” domin bawa al’umma damar tattauna batutuwa da suka shafi siyasa da zaben shekara ta 2019.

Shafin na “Nigeria for Buhari Project 2019” kamar yadda mawallafin sa Malam Zubairu Dalhatu Malami ya bayyana zai bawa magoya bayan Muhammadu Buhari damar tattaunawa batutuwa da suka shafi gwamnati da siyasa gami da karbar ra’ayoyi da tattara bayanai akan takarar shugaba Muhammadu Buhari a 2019.

Shafin na “Nigeria for Buhari Project 2019” a cewar mawallafin sa daidai yake da sauran shafukan sada zumunta da suke a yanar gizo-gizo kamar su Facebook da sauran su. Ya kara da cewa masu amfani da shafin zasu iya dora abubuwa irinsu hotuna da bidiyo gami kirkirar makala da kuma tattaunawa da juna.

Mawallafin yayi nuni da cewa wannan shafi ba’a bude shi ba don ya zama cin zarafi ga wani ko wasu al’umma. Daga karshe yayi addu’ar samun zaman lafiya da kaddamar da zabe cikin kwanciyar hankali a shekara mai zuwa.

33664total visits,2visits today


Karanta:  Jam'iyyar PDP na baikon Atiku Abubakar

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.