An Kaddamar da Shafin Softuwayar Hausa Irinsa Na Farko a Kano

A Kano cikin tarayyar Najeriya masana harshen Hausa da al'adun Hausawa da dalibai daga kasashen Nijar, Togo,Senegal da Mali suka hallara inda suka kaddamar da shafin softuwayar Hausa domin yin anfani dashi a kafar sadarwa ta zamani

A karshen mako ne aka kaddamar da shafin softuwaya na Hausa irin sa na farko a Kano da nufin rayawa da bunkasa harshe da kuma al’adun Hausawa a duniya ta hanyar amfani da kafofifn sadarwar zamani na intanet.

Manazarta da bincike kan harshen Hausa daga Jami’o’i da sarakunan gargajiya da dalibai kan ilimin harshen Hausa daga kasashen Nijar da Togo da Senegal da kuma Mali ne suka halarci taron wanda ya wakana a cibiyar harkokin bincike da bada horo kan lamuran demokaradiyya ta gidan Marigayi Malam Aminu Kano.

Injiniya Abubakar Tsangarwa shine ya kirkiro wannan sabuwar Softuwayar ta harshen Hausa zallla.

Farfesa Bube Namaiwa Masanin tarihi da falsafa ne dake koyarwa a guda daga cikin Jami’o’in kasar Senegal ya bayyana muhimmancin wannan sabuwar softuwayar wajen bunkasa harshen Hausa.

Sarkin Zangon Lome a Togo Mai Martaba Mamudu Salihu Babakeke na biyu , yace sarakunan gargajiya zasu dafa wajen ganin yara masu tasowa sun rungumi sabuwar fasahar domin sanin harshe da al’adun iyaye da kakanni.

Wannan sabuwar fasahar dai ta zo a dai dai lokacin da manazarta ke cewa, amfani da kafar sadarwa ta zamani na kwashe kimanin 70% na lokacin matasa a kowace rana.

Asalin Labari:

VOA Hausa

1246total visits,1visits today


Karanta:  An yi garkuwa da tsohuwar ministar muhalli

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.