An kai karar Trump kan hana wasu shiga Twitter

A shekara 30 da ta wuce an kai shugaban kasar Amurka Donald Trump kara kotu sau 4,000.

Yanzu an kara kai shi kotu bayan da wasu mutum bakwai sun kai kararsa sakamakon toshe su da ya yi daga tofa albarkacin bakinsu a shafinsa na Twitter.

Mr Trump yana amfani da Twitter sosai wajen yabon masoyansa da kuma mayar da martani ga masu sukarsa.

Wata cibiya mai goyon bayan ‘yancin fadin albarkacin baki a jami’ar Colombiya ce ta shigar da karar.

Mutum bakwai din da ke da hannu wajen kai karar sun ce Mista Trump din ne ko kuma ma’aikatansa suka toshe su daga shiga shafin Twitter din shugaban, bayan sun yi ta sukarsa tare da yin izgili kan wani rubutu da ya wallafa a shafin.

Idan aka toshe mutum daga shiga shafin Twitter din wani, to ba zai iya gani ko amsa abin da mai shafin yake wallafawa ba.

Korafin da mutanen suka shigar a karar shi ne cewa, Mista Trump ya haramta musu shiga cikin tattaunawar da ake a shafin nasa kan batutuwan da suka shafi kasa.

Cibiyar ta kira wannan lamari da cewa, ‘kokarin danne hakkin marasa karfi ne,’ a wajen da kowa yake da ‘yancin magana, kuma tauye hakkin damar da suke da ita ne ta ‘yancin fadin albarkacin baki.

Asalin Labari:

BBC Hausa

690total visits,1visits today


Karanta:  Sanatocin Amurka sun soki Twitter

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.