An kama masu garkuwa da mutane a Kano

Hukumomi a Najeriya sun ce sun kama wasu mutane da ake zargi da satar mutane don neman kudin fansa a jihar Kano wanda take arewa maso yammacin kasar.

A wata sanarwa da hukumar bincike ta farin kaya ta Najeriya (DSS) ta aike wa BBC ta ce an kama mutanen da ake zargi da sace mutanen ne a karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano.

“An kama Jolly David da Iliya Alhaji Muhktar da Usha’u Hassan da kuma Muazu Usman a jihar Kano,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Har ila yau, sanawar ta ce ana ci gaba da bincike kan wasu da aka kama bisa zargi da satar mutane wadanda aka bayyana sunansu da Rabiu Sani da Abukakar Sani wadanda aka kama a kan hanyar Zariya zuwa Funtuwa a jihar Kaduna.

Hakazalika an cafke wasu da ake zargi da aikata miyagun laifuka a kasar ciki har da masu garkuwa da mutane a jihohin Nasarawa da Imo da kuma Abia.

Satar mutane don neman kudin fansa tana daya daga cikin manyan matsalolin tsaro da suke ci wa kasar tuwo a kwarya.

Asalin Labari:

BBC Hausa

426total visits,1visits today


Karanta:  'Mutumin Da Ya Yi Wa 'Yarsa Ciki Sau Uku A Kano'

Leave a Reply

Your email address will not be published.