An Kama Mutane Biyu Saboda Lalata Da Kananan Yara

‘Yansanda sun kama wani mutum mai suna Maiwada Ibrahim mai shekaru 43 mazaunin unguwar Lambun Danlawal cikin Katsina bisa zargin aikata luwadi da wasu kananan yara maza biyu kan kudi N400.

Dama can an taba kama wanda ake zargin kan irin wannan laifin a cewar kakakin ‘yan sandan jihar DSP Gambo Isah.

Isah yayi karin bayani da cewa daya daga cikin yaran ne ya kai rahoton faruwar lamarin ga iyayensa, inda daga baya su kuma suka fadawa ‘yan sanda inda suka ce “Wanda ake zargin ya gayyaci yaran ne gidansa ya bawa kowannensu N200 bayan ya gama aikata laifin.”

Ya kuma ce wanda ake zargin na saka musu finafinan batsa a cikin gidan, bayan sun gama kallon sai ya aikata laifin dasu, ya kara da cewa “Da zarar an kammala bincike za a mika wanda ake zargin kotu.”

A wani lamarin daban irin wannan, an kama wani mutum mai shekaru 30 da haihuwa mai suna shamsu Muhammed dan unguwar Barhim dake cikin garin Katsina bisa laifin lalata da wani karamin yaro

Isah ya ce maihafiyar yaron, Hasiya Aliyu wadda ta kai rahoton faruwar lamarin ga ‘yan sanda nata dawainiya da yaron tsahon watanni 18 saboda raunin da aka jiwa yaron lokacin faruwar lamarin.

Yace za a mika wanda ake zargin shima a  kotu.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

5334total visits,3visits today


Karanta:  Dan Shekara 32 Ya Amsa Laifin Yiwa Yarinya ‘Yar Shekara 8 Fyade A Minna

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.