An kama ”yan luwadi 42′ a Legos

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas a Najeriya ta ce ta kama wasu maza guda 42 da ake zargi da luwadi.

An dai kama mutanen ne a wani otal, bayan da rundunar ta kai wani samame sakamakon samun bayanan sirri kan abun da mutanen ke aikatawa.

Yanzu haka rundunar ta ce za ta gurfanar da su a gaban kuliya ranar Litinin.

Neman jinsi guda a Najeriya dai abu ne da ya saba wa al’ada da addinin ‘yan kasar.

Auren jinsin guda kuma ya haramta a dokar kasar, tun lokacin da gwamnatin tsohon Shugaban kasar, Goodluck Jonathan ya rattaba hannu kan hakan.

Sai dai wasu masu rajin kare hakkin ‘yancin bil’adama na cikin gida da waje na sukar irin matakan da hukumomi ke dauka kan masu luwadi da madigo.

Asalin Labari:

BBC Hausa

519total visits,1visits today


Karanta:  Sojin Najeriya zasu fadada atasaye zuwa Kudu maso yammacin kasar

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.