An Kashe Kwamandan Maharban Adamawa Bukar Jimeta a Artabu Da Boko Haram

Rahotanni sun ce sama da mayakan Boko Haram 100 ne su ka yi wa garin Dagu da ke yankin Askira Uba kawanye, garin da ke kan iyakar jihar Adamawa da Borno, lamarin da ya haifar da artabu tsakanin mayakan da wasu maharba har ya kai ga mutuwar wani babban kwamandan maharban.

Bukar Jimeta

Rahotanni daga arewa maso gabashin Najeriya na cewa mayakan Boko Haram sun kashe kwamandan maharban jihar Adamawa, Bukar Jimeta, bayan wani artabu da aka yi a kusa da garin Dagu dake kan iyakar jihar da Borno.

Kwamanda Jimeta ya rasa ransa ne bayan da suka kai dauki a garin na Dagu wanda Boko Haram ta kai wa hari.

Har ila yau harin ya yi sanadin mutuwar wasu maharba uku, amma bayanai sun yi nuni da cewa ‘yan Boko Haram su ma sun rasa mayakansu da dama.

“Ana gumurzun wuta shi kwamandanmu mai suna Bukar Jimeta sai aka same shi (da harbi) da Umar da wani yaro ana ce mashi Musa… wani bafilatani da dansa suma harin ya rutsa da su. Bukar Jimeta ya yaki a ko ina, ba a taba cin nasara a kansa ba.” In ji wani wanda ya tsira da ransa daga wannan hari a wata tattaunawa da suka yi da wakilinmu Ibrahim Abdulaziz.

A cewar wanda aka yi wannan artabu a kan idonsa, harsashi ne ya kare masu.

“Musayar wuta aka yi kaya (harsashi) ya kare, shi kwamanda ya nuna ba zai ja da ba yaba, wadanda suka karaya suka ce tun da ba mu da kaya mu janye, sai ya ki amincewa, garin haka kuma sai Allah ya yi karar kwana.”

Mayakan na Boko Haram su fiye da 100 ne, sanye da kayan sarki dauke kuma da muggan makamai suka kai wannan hari a cewar wadanda suka shida lamarin.

“Allah abin godiya, ajali ne kuma dole ya faru a kan kowa, mu a shirye mu ke har yanzu babu fashi muna kan bakarmu.” In ji shugaban kungiyar Maharba na jihohin Arewa maso gabashin Najeriya, Alh.Muhammad Usman Tola.

Karanta:  Dawowar Buhari ta karo karfin gwuiwa - Gwamna Bello

Bukar Jimeta na cikin kwamandojin maharba da ke tallafawa sojoji a yaki da masu ta da kayar baya na Boko Haram kuma an soma fafatawa da shi, tun a 2014, lokacin da Boko Haram suka kwace wasu kananan hukumomin jihar Adamawa.

Asalin Labari:

VOA Hausa

1148total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.