An Kirkiri Kungiyar Hangen Nesa Ta Tallafawa Lafiya Wato ‘’Visionary for Sustainable Health Support Foundation’’ (VSHSF)

An kirkiri kungiyar hangen nesa ta tallafawa lafiya  wato ‘’Visionary for Sustainable Health Support Foundation’’ (VSHSF).kungiyace mai zaman kanta kuma aka samar daita bada nufin samun riba ba,a shekara ta 2017 karkashin jagorancin Muslim Musa Kurawa tare da hadin gwiwar abokan karatunsa.
Manufar shirin shine tallafawa jamaa da irin abubuwan da  ya koyo a zaman da yayi a kasashen turai lokacin karatunsa da yayin karatun digirinsa na biyu  a fannin lafiyar alumma, wato public health
Musamman ta shirya gangamin wayar da kai daban daban da suka shafi kiwon lfy.musamman ma ga sansanonin yan gudun hijira.

Daya daga cikin taron wayar da kan al’umma akan samun ingantacciyar Lafiya tare da gudanar da gwaje-gwaje
Hakazalika, masu ruwa da tsaki a cikin gungiyar sun kunshin kwararrun likitoci (Epidemiologists, medical lab scientist, public health practitioners) duk sun zuba jari a cikin kungiyar.
Makasudin bude wannan kungiyar ta VSHSF shi ne  don aikin tukuru da wayar da kan al’uma a kan samun ingantatciyar lafiya a kyauta.An tanadi kyakyawan tsarin duba marasa lfy wadanda ke fama da chututtuka daban daban kyauta.tare gudanar da gwaje-gwaje.
 Kungiyar tana da niyyar kyutattawa al’umar karkara da samar musu taimakon gaggawa, saboda asamu raguwar mutuwar masu juna biyu  yayin haihuwa da kuma kananan yara,duba ga hakan ke cigaba da kasancewa babar matsala a arewacin kasarnan.
Kungiyar zata zama wurin  hadinkan mutane. A Kungiyar ta VSHSF mun yarda ‘’ lafiya jari ce’’  wannan shine muhimmiyar rawa da kungiyar zata taka ga al’umma baki daya.
Zakuma mu samar da damarmaki iri-iri ga matasanmu dake  da nufin shiga ayyuka sakai da wayar da kai kan harkokin  kiwon lfy da samar da cigaban alumma.

Shugaban Kungiyar Mr. Muslim Musa Kurawa da matamakin sa Dr. Bashir Umar
Domin neman bada gudurmuwa ko tallafawa wannan kungiya.a nememu ta
07032457007
Twitter> vshs_foundation
Instagram> vshs_foundation

 

Asalin Labari:

Muryar Arewa

1723total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.