An lakadawa ‘yan majalisar Venezuela duka

An yi wa ‘yan majalisar jina-jinaREUTERS

Masu goyon bayan gwamnatin Venezuela sun kutsa kai cikin majalisar dokokin kasar inda suka yi wa ‘yan majalisar da ‘yan jarida duka.

Ganau sun ce lamarin ya faru ne bayan ‘yan majalisar sun gama kada kuri’a kan bikin kewayowar ranar samun ‘yancin kan kasar.

Masu kutsen sun shiga majalisar dauke da sanduna sannan suka tashi abubuwan da ke sa tartsatsin wuta a ginin majalisar, in ji kamfanin dillacin labarai na AFP.

Hotunan da aka dauka sun nuna yadda ‘yan majalisa na jam’iyyun hamayya suka yi jina-jina.

Wani shafin intanet da ke goyon bayan ‘yan hamayyar Venezuela La Patilla ya bayar da rahoton cewa ‘yan daba sun kai hari kan ‘yan majalisar a a ginin majalisar da ke Caracas.

Ya kara da ce “Magoya bayan gwamnatin sun yi wa mutane da dama rauni a cikin majalisar”.

Wata ‘yar majalisa Yajaira de Forero ta ce an raunta uku daga cikin abokan aikinta, ciki har da wanda aka kai asibiti.

Dan majalisa daga jam’iyyar hamayya Americo de Grazia na ciki wadanda suka jikkata.

Wasu rahotanni sun ce mutum takwas aka jikkata.

Asalin Labari:

BBC Hausa

210total visits,1visits today


Karanta:  Amurka Tana Tunanin Ko Ta Dauki Matakin Soja Kan Venezuela

Leave a Reply

Your email address will not be published.