An Mayar Da Sunan Jami’ar ‘Northwest’ Zuwa Maitama Sule

Jami’ar Nothwest

Gwamnatin Jihar Kano ta bada sanarwar mayar da sunan Jami’ar NorthWest da ke Kano zuwa Jami’ar Maitama Sule domin tunawa da marigayin wanda ya rasu a radar Litinin.

An gudanar da jana’izar Dr. Yusuf Maitama Sule, Dan Masanin Kano da yammacin ranar Talata ne bayan da jirgin da ke dauke da gawarsa ya sauka a filin tashi da sauka na Mallam Aminu Kano dake Kano. Dubun dubatar mutane daga sane da cikin jihar suka tarbe ta, wadanda suka hada da gwamnonin Kano, Jigawa, Bauchi, Katsina da kuma Sokoto.

Jana’izar wadda aka gabatar a Kofar Kudu ta fadar Mai Martaba Sarkin Kano wadda babban limamin Kano Farfesa Sani Zahradeen ya sallata. Cikin wadanda suka halarta sun hada da Mai Marcaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II da shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki, Ministan harkokin cikin gida Abdulrahman Dambazau, Ministan Tsaro Mansir Dan Ali da saurian banyan jami’an gwamnatin tarayya dana jihojhi.

An binne Marigayi Dr. Yusuf Maitama Sule a makabartar Kofar Mazugal dake cikin birnin Kano.

802total visits,1visits today


Karanta:  Kamaru: Wasu Dalibai Sun Kauracewa Komawa Karatu

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.