An Roki Nakasassu A Jihar Borno Da Su Kaurace Wa Bara.

Gwamnatin jihar Borno ta bukaci nakasassu a jihar da su jingine sana'ar bara su rungumi sana'oi, kwamishinan mata da walwalasr matasa ne MadamPanta Baba Shehu tayi wannan kiran.

Gwamnatin jihar Borno tayi kira ga nakasassu a jihar da suyi wa Allah Da Ma’aikainsa su daina barace-barace akan tituna.

Wannan kiran ko ya fito ne daga bakin kwamishinar harkokin mata da Walwalar matasa Malama Panta Baba Shehu, kuma tayi kiran ne sai’lin da take rarraba kayan abinci mai tarin yawa ga nakassassun.

Tace gwamnati ta samar da wurin koya musu sana’a wanda za’a bayan shi kungiyar Boko Haram ta lalata shi.

Shiko a nasa jawabi kakakin kungiyar Nakasassun, Ibrahim Musa yace jifar matattar magen da akayi da su ne ya jefa su cikin halin bara.

Asalin Labari:

VOA Hausa

273total visits,1visits today


Karanta:  Wata Mata Ta Kashe Kanta Saboda Mijinta Zai Yi Mata Kishiya

Leave a Reply

Your email address will not be published.