An sake kai hari Jami’ar Maiduguri

Rahotanni dake fitowa daga birnin Maiduguri na Jihar Borno, na cewa ‘yan kunar bakin wake sun sake afkawa cikin Jami’ar Maiduguri, inda biyu daga cikinsu suka tashi wani abu mai fashewa dake jikinsu.

Al’amarin ya faru ne da misalin karfe 11:50 na daren Alhamis, a inda wasu da suka shaida lamarin sun ce wasu mutane su uku da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka kutsa cikin Jami’ar. Bayanai sun tabbatar cewa biyu daga cikinsu sun tashi bama bamai da ke jikinsu, inda nan take suka rasa rayukansu.

Majiyar ta ce, hake ya janyo hankalin jami’an tsaro dake cikin Jami’ar inda suka yi yunkurin dakile harin, inda suka harbe mutum na ukun wanda yayi yunkurin tserewa.

Kawo yanzu dai babu wani rahoto na asarar rayuka baya ga na maharan.

595total visits,1visits today


Karanta:  Kano Ta Tantance Masu Girka Abinci 11,000 Don Shirin Ciyar Da Abinci A Makarantu

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.