An Saki Tsohon Firaministan Libya Da Aka Sace

Tsohon Firaministan Libya Ali Zeidan ya samu kan sa bayan kwashe kwanaki 9 a hannu wata kungiya da ta yi garkuwa da shi a birnin Tripoli lokacin da ya kai ziyarar farko zuwa birnin a cikin shekaru 3.

Tsohon Firaministan Libya Ali Zeidan ya samu kan sa bayan kwashe kwanaki 9 a hannu wata kungiya da ta yi garkuwa da shi a birnin Tripoli lokacin da ya kai ziyarar farko zuwa birnin a cikin shekaru 3.

Karam Khaled wani na kusa da shi ya ce yana cikin koshin lafiya bayan sace shi da ‘Yan bindigan suka yi a otel din sa ranar 13 ga watan nan.

Zeidan mai shekaru 77 ya rike mukamin Firaminista tsakanin watan Nuwamban 2012 zuwa Maris na 2014 da aka tsige shi akan zargin fatali da kudaden jama’a

Babu dai wani cikakakken bayani akan mayakan da suka sace shi amma Mista Zeidan ya zargi mayakan da ke biyayya ga gwamnatin Libya da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya.

Halin tsaro a Libya na ci gaba da tabarbarewa saboda rashin tsayayiyar gwamnati a kasar.

Asalin Labari:

RFI Hausa

269total visits,1visits today

Karanta:  Amurka za ta ladabtar da kwamandan sojan ruwanta

Leave a Reply

Your email address will not be published.