An samu fashe-fashen bama-bamai a Maiduguri

Akalla mutane kusan goma sha daya (11) suka rasa rayukansu a was tagwayen fashewar abubuwa wadanda ake zargin bama-bamai ne, a ranar Talata da daddare a birnin Maiduguri.

Wata majiya mai karfi ta tabbatar da cewar fashewar abun na farko da na biyu, ya faru ne daidai karfe 9.45 na dare a Mulaikalmari, kilomita shida daga wajen Maiduguri.

Majiya ta bada bayanin cewar mutane takwas wadanda suka hada da Dan Kunar Bakin waken suka mutu.

Hakazalika, wasu mutane uku tare da wasu biyar, sun rasa rayukansu a fashewa ta hudu, wadda ta afku mintuna ashirin bayan faruwar wadancan, a yankin Polo-Sabon gari dake birnin Maidugurin a cewar majiyar wadda suka taimaka wajen kawar da gawawwakin wadanda ta rusta da su.

Shugaban hukumar agajin gaggawa ta jiha, Alhaji Satomi Ahmed, ya tabbatar da kai harin. Satomi ya kara da cewar, tuni aka aika da ma’aikata wajen da al’amarin ya faru domin bada agajin gaggawa.

 

 

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Omojuwa.com

3468total visits,2visits today


Karanta:  Hukumar Tashar Jiragen Ruwa Ta Sake Gina Wasu Makarantun Sakandare a Borno

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.