An sulhunta rikicin dake tsakanin Nafisa Abdullahi da Hadiza Gabon

– An shawo kan rikicin da ya shiga tsakanin Nafisa Abdullahi da Hadiza Gabon

– Rikicin nasu ya faro ne tun a jihar Kaduna yayin da suke dandalin shirya fina finai

A jiya Alhamis 20 ga watan Afrilu ne kungiyar mashirya fina finai na Kannywood suka shiga tsakanin jaruman yan fim din nan su biyu Nafisa Abdullahi da Hadiza Gabon bayan wata arkalla data shiga tsakaninsu.

Shaidan dai ya shiga tsakanin jarumai matan ne a jihar Kaduna yayin da suke bakin aiki wajen shirya wani fim a garin na Kaduna, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.

Sai dai kungiyar mashirya finafinan Kannywood, MOPPAN tace ba zata zura idanu ‘ya’yan ta suna fada da juna ba, hakan ta sanya su shiga tsakanin sulhunta su. Daga karshe an hangi jaruman biyu suna murmushi tare da rungumar juna.

Asalin Labari:

NAIJ

5069total visits,10visits today


Karanta:  Ashe ba a dakatar da Rahama Sadau daga Kannywood ba?

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.