An tantance sabbin hakimai da dagatai 230 a Kaduna

Gwamnatin Kaduna da ke arewacin Najeriya ta ce ta mutum 230 domin zama hakimai da dagatai a yankuna 77 na jihar.

Wata sanarwa da kakakin Gwamna Nasir El-Rufai , Samuel Aruwan ya fitar ya ce gwamnati ta yanke shawarar dawo da yankuna 77 kamar yadda suke gabanin 2001.

A cewarsa, gwamnati ta dauki matakin ne bayan majalisar zartarwa na jihar ya amince da rahoton wani kwamiti da aka nada domin duba yadda hakimai da dagatai ke gudanar da mulkinsu.

“Taron da majalisar zartarwa ta yi ranar 24 ga watan Afrilu ya gano cewa ba a bi wasu ka’idoji masu inganci ba wajen kara masarautu daga 77 zuwa 390 ba. Hasalima ‘yan siyasa ne suka yi hakan domin dora nauyin masarautu 313 kan kananan hukumominmu kuma hakan ya rage kimar hakiman”, in ji Gwamna Elrufai.

A cewar sanarwar, ranar 25 ga watan Afrilu gwamnan jihar ya tuntubi majalisar sarakunan gargajiya wacce ta bukaci a ba ta mako biyu domin tattaunawa kan batun sannan ta mika rahoto.

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce daga karshe majalisar sarakunan ya goyi bayan sake fasalin masarautun hakimai da dagatai kuma hakan ne ya sa gwamnati ta aiwatar da matakin.

A watan jiya ne gwamnatin ta soke daruruwan hakimai da dagatai da kuma masu unguwanni, tana mai cewa an kirkiro su ne ba bisa ka’ida ba kuma suna lashe makudan kudi.

Asalin Labari:

BBC Hausa

2836total visits,1visits today


Karanta:  Ana daf da wancakali da Kuraye da Diloli daga Gwamnati - Aisha Buhari

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.