An Tsaurara Matakan Tsaro A Kano

Jami’an Tsaro sun tsaurara matakan tsaro a Kano saboda bukukuwan Babbar Sallah da za a fara yau din nan.

A sanarwar da Rundunar ‘Yan Sandan Jihar ta fitar jiya wadda Shugaban Hurda da Jama’a Magaji Musa Majia, ya sanyawa hannu, cewa yayi an dauki matakan tsaron da suka kamata don ganin anyi bukukuwan sallar lafiya.

Inda yace”Munyi kyakykyawan shiri, mun samar da isassun jami’an tsaro, da jami’an sintiri a guraren ibada, guraren shakatawa, kasuwanni, kofofin shige da fice da sauran muhimman gurare don ganin anyi bikin sallah lafiya”.

Mai Magana da Yawun ‘Yan Sandan ya shawarci masu zuwa wajen ibadah da kada su halarci wajajen ibadar da duk wani abu da rike shi bai zama dole face shinfidun sallah.

Majiyan ya kuma ummarci iyaye da kada su kyale yaransu tafiya su kadai ba tare da an sami wanda zai raka su unguwa ba a daukacin bukukuwan sallar don rage yawaitar batan yara.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

485total visits,2visits today


Karanta:  Ana bincike ko cutar kyandar birrai ta je Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.