An tsinci gawar yara 3 a cikin wata mota a jihar Kaduna

Rundanar ‘yan sanda ta na bincike akan gawar wadansu yara uku ‘yan gida daya da aka tsinta a cikin wata mota a jihar Kaduna A can jihar Kaduna ne aka tsinci gawar wasu yara guda uku ‘yan gida a cikin wata mota, inda har yanzu a ke binkicen sanadiyar mutuwar ta su.

Rahotanni daga shafin BBC sun ruwaito cewa, iyayen yaran wadanda mazauna unguwar Tudun Wada ne a jihar ta Kaduna sun bayyana cewa, tun a ranar larabar makon da ya gabata ne suka nemi yaransu guda hudu su ka rasa.

Wani daga cikin mahaifin yara biyu daga ciki, Suleiman Hashim, ya bayyana cewa kwanaki uku suka yi wajen neman wadannan yara; Hamza, Ikram,Ilham da Raihan wanda duk cikin su babu wanda ya haura shekaru uku da haihuwa.

Sai a ranar asabar ne su ka tsinci gawar wannan yara a cikin wata motar makwabcinsu duk sun rasu in banda Ilham, wadda a halin yanzu tana karbar kyakkyawar kulawa a asibiti.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar su na nan a bakin aiki don gano sandiyar mutuwar wannan yara don tsananta bincike.

Asalin Labari:

NAIJ Hausa

1536total visits,2visits today


Karanta:  'Yan Kunar bakin wake sun kashe mutane 12

Leave a Reply

Your email address will not be published.