An yi hatsaniya yayin zanga-zangar Dino Melaye

An samu hatsaniya yayin da wasu mutane suke zanga-zangar nuna goyon baya ga Sanata Dino Melaye, mai wakiltar jihar Kogi ta yamma a majalisar dattawan Najeriya.

Hargitsin ya fara ne yayin zanga-zangar da wasu ke cewa sanatan ne ya shirya, inda gwamnatin jihar take zargin cewa an kashe mutum daya.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne ranar Litinin a gaban kwalejin kimiyya da fasaha, mallakar jihar Kogi da ke Lokoja a lokacin da sanatan da magoya bayansa suka hallara domin gudanar da zanga-zangar nuna masa goyon baya “saboda kiranyen da ake son a yi masa daga majalisa”.

Hatsaniya ta kaure ne tsakanin magoya bayan sanatan da magoya bayan Gwamnan Jihar Yahaya Bello, kamar yadda wasu rahotanni suka ce.

Sanata Dino Melaye ta shafinsa na Twitter ya tabbatar da cewa an samu musayar harbe-harbe kuma ya gode wa Allah bayan da ya tsira da ransa. “Ba zan iya sanin ko wani ya mutu ba, amma na ga mutum biyu da suka ji rauni,” in ji shi.

Sai dai bai yi karin haske ba kan abin da ya jawo harbe-harben.

An dade dai an takun saka tsakanin sanatan da gwamnan jihar.

Asalin Labari:

BBC Hausa

355total visits,3visits today


Karanta:  Fadan Ranar Hawan Daushe: An Gargadi Matasa Kan Rigingimun Siyasa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.