An Yi Jana’izar Dr. Maitama Sule

An gudanar da Jana’zar Dr. Yusuf Maitama Sule, Dan masanin Kano

Da yammacin yau Talata ne jirgin dake dauke da gawar Marigayi Dr. Yusuf Maitama ya sauka a filin jirgin sama na Kano, dubun dubatar mutane ne sukaje domin tarbar gawar marigayin, wadanda suka hada Gwamnonin Kano, Jigawa, Bauchi, Katsina da kuma Sokoto.

An gudanar da Jana’iza a kofar Kudu ta fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Wanda Limamin Kano Farfesa Sani Zaharaddin ya sallaci gawar. Mutane da dama ne daga ciki wajen kano suka halarci sallar Jana’izar Cikinsu harda Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na II da shugaban Majalisar Dattijai Bokola Saraki, Ministan cikin gida Abdurrahaman Danbazau da Ministan tsaro Mansir Dan Ali da kuma manyan Jami’an gwamnatin tarayya da na Jahohi.

An binne Marigayin a makabartar Kofar Mazugal dake cikin birnin Kano.

457total visits,1visits today


Karanta:  Ana Zargin Wani Dan Sanda Da Kashe Kansa Saboda Sauya Masa Gurin Aiki Zuwa Maiduguri, ‘Yan Sanda Sun Karyata Zargin

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.