Ana daf da wancakali da Kuraye da Diloli daga Gwamnati – Aisha Buhari

Uwargidan Shugaban kasa Aisha Buhari ta ce an kusa korar Kuraye da Diloli daga Gwabnatin Buhari. Aisha Buhari ta fadi wannan maganar ne a shafinta na Facebook ranar litinin inda ta yi amafani da abinda Sanata Shehu na jihar Kaduna ya rubuta yana habaici ga wasu ‘yan siyasa.

Uwargida Aisha ta fadi wannan maganar ne bayan dawowa daga duba maigidanta a makon jiya daga London, ta fadi hakan ne saboda tana zargin wasu na farautar kujerar maigidanta da ke jinya a kasar Ingila, mutane da yawa suna ganin wannan maganar ta martini ce ko kuma gugar zana.

Har yanzu dai Shugaba Buhari yana jinya rashin lafiyar da yake yi a kasar Ingila, sannan mukaddashinsa Yemi Osibanji shike gudanar da mulkin Najeriya a yanzu.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, BBC Hausa

3730total visits,1visits today


Karanta:  Korea ta Arewa Ta Yi Wancakali Da Barazanar Trump

Leave a Reply

Your email address will not be published.