Ana Neman Hanyoyin Da Za’a Inganta Makarantun Allo.

Wata kungiya mai zaman kanta da hadin gwiwar 'yan jarida na tattaunawa akan hanyoyin da za abi domin inganta makarantun allo a arewacin Nigeria.

Gidauniyar nan da ake kira NEEM ta shirya wani taro na musammam da ‘yan jarida domin musayar ra’ayi akan yaddasukan za a inganta makarantun allo a fadin arewacin Nigeria.

Daya daga cikin burin iyayen yaran nan masu karatu a irin wadanan makarantun shine yaran su haddace Al-kura’ni mai tsarki.

To amma kuma sau tari sai a samu akasin haka, domin sai daliban su rikide su zame wani abu na daban, wata sa’a ma zame barazana ga al’ummar kasa ko kuma su kama barace-barace.

Malam Asharaf Kabiru Usman shine babban Jami’in gidauniyar kuma ya shaidawa wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari dalilin su na neman tattaunawa da ‘yan jarida kan wannan batu.

Asalin Labari:

VOA Hausa

340total visits,1visits today


Karanta:  An Gurfanar da Malamin Makaranta Saboda Zargisa da Lalata da ‘Yan Mata 3 ‘Yan Uwan Juna

Leave a Reply

Your email address will not be published.