Shugaba Buhari zai dawo nan da mako biyu — Rochas

Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo ya bayyana cewa nan da mako biyu Shugaba Kasa Muhammadu Buhari zai koma gida daga jinyar da yake yi a birnin London.

Gwamna Rochas Okorocha wanda yana daya daga cikin gwamnoni hudu da suka ziyarci shugaba Buhari a birnin na London ya shaida wa a yau BBC cewa “muna ganin daga nan zuwa sati biyu insha Allah zai koma gida ya ci gaba da aikinsa”.

Gwamna Rochas ya kara da cewa shugaban yana cikin koshin lafiya “kuma zancen da ake yi cewa yana cikin mawuyacin halin ba gaskiya ba ne. Yana nan lafiya lau.”

“Na yi mamakin yadda na gan shi. Yana da koshin lafiya. Abubuwan da ake cewa game da rashin lafiyarsa ba haka muka gani ba,” in ji gwamnan na jihar Imo.

Asalin Labari:

Muryar Arewa da BBC Hausa

628total visits,1visits today


Karanta:  Bankin Raya Afrika Zai Zuba Jarin Bunkasa Aikin Noma a Afrika

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.