APC Ta Kira Aisha Alhassan Dangane Da Maganganun Da Tayi Akan Buhari

Daga Abuja: Jam’iyya mai mulki a kasa wato APC ranar Alhamis ta kira Ministan Mata Hajiya Aisha Alhassan dangane da maganganun da tayi  kan wanda zata marawa baya a zaben shugaban kasa mai zuwa na shekarar 2019.

Ministan wadda ta isa sakatariyar jam’iyyar ta kasa da misalin karfe 1:45 na yamma an wuce da ita kai tsaye zuwa ofishin shugaban jam’iyyar na kasa wato John Odigie-Oyegun inda suka tattauna su kadai a asirce.

Idan za a iya tunawa dai ministan ce ta fara haifar da yanayin da ake ciki inda kwanan baya tayi hira da kafafen yada labarai inda karara ta nuna goyon bayanta ga daya daga cikin jigon jam’iyyar kuma tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar maimakon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kamfanin jaridar vanguard ya fahimci cewa jam’iyyar APC na jan kafa gurin shiga tsakanin kan lamarin don kuwa gwamnatin da Buharin ke jagoranta har yanzu bata dauki matsaya ba kan ko zata hukunta ministan ko akasin hakan.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Vanguard

449total visits,2visits today


Karanta:  Kwankwaso yana nan daram a jam'iyyar APC

Leave a Reply

Your email address will not be published.