APC ta mayar wa Buba Galadima martani

Jam'iyyar APC karkashin shugabancin Adams Oshiomhole ta ce tana kokarin sasantawa da bangaren da ya ware ya kafa wani bangare da suka wa lakabi da Reformed APC, ko sabuwar APC.

A ranar Laraba ne wasu jiga-jigan APC da suka hada da ‘yan bangaren sabuwar PDP suka yi wani taro a Abuja, inda suka bayyana Injiniya Buba Galadima a matsayin shugabansu.

Sakataren Walwala na jam’iyyar APC Ibrahim Kabir Masari ya ce hakan ba wani abu ba ne illa fushi ne na ‘yan gida daya kuma suna kokarin sasantawa da su.

Ya ce ko a ranar Laraba sai da bangaren Oshiomhole ya kai ziyara majalisar dattawa, inda suka gana da bangaren da ya yi fushi.

“Abin da ya faru ba wai rikici ba ne sai dai kawai na ce bacin rai bisa ga wadansu al’amurra wadanda mutum yake ganin an yi masa ba daidai ba. Kuma muna kokarin sasanta abin, ” in ji shi.

An dade ana takun-saka tsakanin wadanda suka shigo jam’iyyar kafin zaben 2015 da ake kira ‘yan sabuwar PDP da kuma bangaren gwamnatin APC.

‘Yan sabuwar PDP sun yi zargin cewa ba a damawa da su a gwamnatin APC tare da barazanar daukar mataki idan har ba a biya bukatunsu ba.

Sannan a wani bangaren kuma ana tafiya ne da sunan jam’iyya daya amma akwai masu hamayya da juna a APC musamman a jihohi da dama da jam’iyyar ke mulki.

An samu bangarorin APC da suka gudanar da nasu zaben shugabannin jam’iyyar na daban a matakin mazabu da kananan hukumomi da kuma jiha.

Bangaren Kwankwasiyya na daga cikin bangarorin APC da suka gudanar da nasu zaben shugabannin jam’iyya a matakin mazabu da kananan hukumomi da kuma jiha.

Sannan tsohon gwamnan na Kano kuma sanata a APC ya kauracewa zaben shugabannin jam’iyyar na kasa da aka gudanar a Abuja.

Karanta:  Osinbajo na shirin yin girgiza a Majalisar Zartarwa

Kwankwaso ya ce zuwansa babban taron na APC na iya haifar da abin kunya da rikici.

Masharhanta siyasa na ganin rigingimun APC da ta ke fama da su na iya yi wa jam’iyyar illa sosai a zaben 2019.

Asalin Labari:

BBC Hausa

41572total visits,4visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.