Atiku: APC Ta Musanta Cewa Ta Bukaci Alhassan Da Tayi Murabus

Sakataren Watsa Labaran Jam’iyyar  APC, Malam Bolaji Abdullahi yace jam’iyyar tasu bata bukaci Ministan Matan, Sanata Aisha Alhassan da tayi murabus ba saboda maganganun da tayi kwanakin baya a kafafen yada labarai.

Ya kuma ce zuwan da tayi sakatariyar jam’iyyar a Abuja ranar Alhamis ba wata gayyata bace ta musamman.

Ministan wadda maganganun da tayi dangane da wanda zata zaba a matsayin shugaban kasa a zaben shekarar 2019 ya tada hazo, sunyi wani zama da shugaban jam’iyyar na kasa a asirce jiya a sakatariyar jam’iyyar.

An dai sha rawaitota sau da dama tana cewa zata marawa tsohon matemakin shugaban kasa Atiku Abubakar baya mutukar dai ya nuna sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2019, inda take bayanin cewa Atikun dama can shi ne Ubangidanta a siyasa.

Bayanan nata sun fuskanci kalubale daga gurin wasu jigajigan jam’iyyar wadanda suka rinka kiranta da cewa batada biyayya kuma tana yiwa Buhari da jam’iyyar zagon kasa haka kuma yakamata tayi murabus ko kuma a sauke ta daga mukaminta.

A karshen ganawar tasu wadda tayi tsahon awanni biyu, ance Alhassan taki bayyanawa ‘yan jarida makasudin zuwan nata sakatariyar jam’iyyar.

Abdullahi ya fadawa manema labarai a Abuja cewa ministan ta gana da shugabanci jam’iyyar ne amma “ba a bukaceta data ajiye mukaminta ba kamar yadda ake yadawa.”

“A’ a hakan ma bata taso ba, abin da mukace muna so shi ne mu fahimci a wane bigire ta fadi abin data fada.

“Amma bai dace ga wanda ke rike da mukami irin nata ba a jam’iyya ya ringa irin wadannan maganganun,” a cewarsa.

Wata majiya dake kusa da shugabancin jam’iyyar ya fadawa manema labarai cewa shugabannin jam’iyyar sun bayyana damuwarsu da rashin jin dadinsu dangane da maganganun na ministan.

Karanta:  Buhari ya yi alla-wadai da harin mujami’a a Najeriya

Acewar majiyar, an fadawa ministan cewa jam’iyyar  bazata taba yadda da ita ba a nan gaba.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, NAN, Vanguard

4047total visits,5visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.