An Damke Masu Safarar Mutane a Yammacin Afirka

Hukumar ‘yansandan kasa-da-kasa (INTERPOL) ta ce an damke masu safarar mutane guda 40 tare da ceto mutane 500 a wani samame a yammacin nahiyar Afirka.

An Damke Masu Safarar Mutane a Yammacin Afirka

Hukumar ‘yansandan kasa-da-kasa (INTERPOL) ta ce an damke masu safarar mutane guda 40 tare da ceto mutane 500 a wani samame a yammacin nahiyar Afirka. Hukumar ta kai wannan samame ne a lokacin da kasashen duniya ke kokawa game da cinikin bayi da aka bankado a kasar Libya. A cikin wata sanarwa da ta fitar, […]

Gwamnatin Nigeria ce ta 35 a Afirka – Gidauniyar Mo Ibrahim

Najeriya tana mataki na 35 a rahoton kididdigar shekara-shekara kan yanayin gwamnatoci a nahiyar Afirka, wanda Gidauniyar Mo Ibrahim ta fitar a birnin Dakar na kasar Senegal ranar Litinin.

Gwamnatin Nigeria ce ta 35 a Afirka – Gidauniyar Mo Ibrahim

Kodayake rahoton ya ce gwamnatin Najeriya ta dan yi aiki a tsawon shekara biyar da suka wuce, kuma ta samu maki 48.1 cikin 100. Sai dai abin da kasar ta samun ya yi kasa da adadin tsaka-tsaki na kasashen yankin Yammacin Afirka wato maki 53.8. Har ila yau Najeriya ta samu maki mai yawa a […]

Musulman Rohingya na Fuskantar Wariya – Amnesty

Kungiyar kare hakkin dan'adam ta Amnesty International ta ce musulmai 'yan Rohingya a Myanmar na fuskantar wani nau'in wariya mai kama da ta launin fata karkashin jagorancin gwamnati.

Musulman Rohingya na Fuskantar Wariya – Amnesty

Rahoton baya-bayan nan na Amnesty ya bayyana kauyukan Rohingya a matsayin kurkukun talala, inda ya al’ummomin suka shafe gomman shekaru suna fuskantar musgunawa. Mai aikowa BBC rahoto daga Kudu maso Gabashin Asiya na cewa rahoton Kungiyar Amnesty daya ne daga cikin takardun da kungiyoyin kare hakkin dan’adam ke tattarawa da yiwuwar shigar da manyan hafsoshin […]

Badaƙalar Biliyan 2.1: Maina Ya Ƙalubalanci EFCC …Ya Ce Yana Bin Gwamnati Bashin Biliyan 159

Maina ya yi wannan ƙalubale ne ta hannun lauyansa, Barista Sani Katu, inda ya ce bai saci ko ficika ba, sai dai ma tulin bashin da yake bin gwamnatin tarayya na Naira Biliyan 159.

Badaƙalar Biliyan 2.1: Maina Ya Ƙalubalanci EFCC …Ya Ce Yana Bin Gwamnati Bashin Biliyan 159

Tsohon Jagoran Fansho, Abdulrasheed Maina ya ƙalubalanci Hukumar EFCC da ta zo a baje zarginsa da ta ke yi kan badaƙalar Naira Biliyan 2.1 a faife. Inda tsohon jagoran fanshon ya ce, a tsarkake yake kuma baya tsoron a yita ta ƙare. Maina ya yi wannan ƙalubale ne ta hannun lauyansa, Barista Sani Katu, inda […]

Korea Ta Arewa na tallafa wa ta’addanci- Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana Korea Ta Arewa a matsayin kasar da ke tallafa wa ayyukan ta’addanci, abin da ya maido da kasar cikin jerin sunayen makiyan Amurka.

Korea Ta Arewa na tallafa wa ta’addanci- Amurka

A lokacin da ya ke ayyana Korea Ta Arewa a matsayin kasa mai tallafa wa ta’addanci a fadar White House, Trump ya ce, tun da jimawa ya kamata su dauki wannan mataki. Korea Ta Arewa na ci gaba da kasancewa cikin jerin takunkuman da Amurka da Majalisar Dinkin Duniya suka kakaba ma ta saboda gwaje-gwajenta […]

Nigeria: Harin kunar bakin wake ya kashe mutane a Mubi

Rahotanni dai sun ce lamarin ya faru ne a wani masallaci da ake kira Masallacin Madina cikin garin na Mubi lokacin da ake sallar Asubah.

Nigeria: Harin kunar bakin wake ya kashe mutane a Mubi

Akalla mutum 21 suka mutu bayan wani ya kai harin kunar bakin wake wani masallacin cikin garin Mubi da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya. Rahotanni dai sun ce lamarin ya faru ne a wani masallaci da ake kira Masallacin Madina cikin garin na Mubi lokacin da ake sallar Asubah. Dan kunar bakin […]

Karin Bayani Akan Harin Mubi

Yanzu an gano cewa dan kunar bakin wake ne yayi shigar burtu ya tada bam a cikin wani Masallaci garin Mubi

Karin Bayani Akan Harin Mubi

Masallacin da dan kunar bakin waken yakai har yau Talata ana kiransa Masallacin Madina a garin Mubi. Kafin a ankara dan kunar bakin waken ya tada bam din dake jikinsa yayinda mutane suke sallar asuba kuma kammala raka’a daya Yawancin mazauna wurin ‘yan kabilar Shuwa ne da suka fito daga jihar Borno sanadiyar rikicin Boko […]

Dubban ‘yan jam’iyar APC sun cika da buri

Dubun-dubatar magoya bayan jam`iyyar APC mai mulki a Nigeria na ci gaba da zaman jiran-tsammani.

Dubban ‘yan jam’iyar APC sun cika da buri

Wannan ya biyo bayan ikirarin da shugaban kasar ya yi na kara yawan ministoci da nade-naden wasu mukamai ta yadda `yan jam`iyyar za su ji ana damawa da su. Abin tambaya shi ne ko gaggauta yin nade-naden zai kara wa shugaban kasa da jami`iyyar APC tagomashi a cikin lokacin da ya rage wa`adin mulkinsa ya […]

Ko Kunsan Kasar Da Ake Damawa Da Mata A Wasan Tamola?

Bisa al'ada wasan kwallon kafa an fi alakanta shi da Maza, amma yanzu mata sun fara nuna sha'awar wannan fanni a Afirka.

Ko Kunsan Kasar Da Ake Damawa Da Mata A Wasan Tamola?

Kamar a kasar Ghana, wasu matasa mata sun yunkuro don shiga a dama da su a fagen wasan kwallon kafa. Sai dai kuma lamarin ka iya fuskantar cikas ta fuskar Addini da al’ada. To amma wasu matan da suka fito daga arewacin kasar ta Ghana, sun toshe kunnensu tare da fara atisaye don ganin burinsu […]

Gwamnan Jihar Neja Ya Kara Korar Kwamishinoninsa

Biyo bayan matsin lambar da gwamnan jihar Neja ke fuskanta daga jam’iyyar sa ta APC bisa sallamar da ya yiwa kwamishanoninsa, gwamnan, Alhaji Abubakar Sani Bello ya fito fili ya bayyan dalilan da suka saya yi waje dasu

Gwamnan Jihar Neja Ya Kara Korar Kwamishinoninsa

Alhaji Abubakar Sani Bello yayi karin haske akan dalilan da suka sa ya kori kwamishanoninsa daga bakin aiki. A cikin hirar da gwamnan yayi da Muryar Amurka yace kowace gwamnati bayan wani dan lokaci “kan yi tankade da rairaya”. Yace abun da aka saba yi suka yi domin su yi wasu gyare-gyare. Dangane da gamsuwa […]