Babu Yadda Boko Haram Zata Habaka Ba Tare da Haramtattun Kudi Ba – Osinbajo

Yayinda yake jawabi a wajen taron kwamitin dake yaki da kudaden haram a yammacin Afirka mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya ce babu yadda Boko Haram zata habaka daga gari daya har zuwa garuruwa da dama a Nigeria da wasu kasashen ba tare da samun haramtattun kudade ba

Babu Yadda Boko Haram Zata Habaka Ba Tare da Haramtattun Kudi Ba – Osinbajo

A wurin taro na goma sha takwas na kwamitin yaki da halasta kudaden haram a yammacin Afirka, Mataimkain Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo yace matsalar halasta kudaden haram na yiwa kasashe irinsu Najeriya barazana. Farfesa Osinbajo yayi mamakin yadda wata bakar akida da ta samo asali a gari daya ta habaka har ta yadu cikin […]

Buhari Ya Taya Jonathan Murnar Cika Shekara 60

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya tsohon Shugaban kasar Goodluck Jonathan murnar cika shekara 60 a duniya.

Buhari Ya Taya Jonathan Murnar Cika Shekara 60

A ranar Litinin ne Mista Jonathan zai cika shekara 60 da haihuwa. Shugaba Buhari ya yaba wa tsohon shugaban inda yake cewa: “ya fara rike mukamin mataimakin gwamna ne, kafin daga bisani ya zama gwamna, kafin ya zama shugaban kasa na tsawon shekara shida, ya fara zama mataimakin shugaban kasa ne”. Daga nan shugaban ya […]

‘An Mayar Damu Saniyar Ware’ — Niger Delta

Wasu Shugabannin a yankin Neja Delta na ci gaba da tofa albarkacin bakin su dangane da barazanar da wasu masu tada kayar baya a yankin suka yi cewa zasu koma farfasa bututan mai a yankin.

‘An Mayar Damu Saniyar Ware’ — Niger Delta

Farfesa Akasoba Zainab Duke-Abiola, matar wani basarake ce a yankin, kuma shugabar wata kungiyar wanzar da zaman lafiya a Najeriya, ta shaida wa BBC cewa, duk da kundin tsarin mulkin kasa ya basu damar su yi bore, ai bai ba su damar su tayar da hankalin jama’a ba. Ta ce abin da ta ke gani […]

An bai wa Mugabe wa’adin sauka daga mulki ko a tsige shi

Tsoffin kawayen shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, sun yi kakkausar suka ga matakin da ya dauka na yin biris da kiraye-kirayen da ake masa a kan ya yi murabus.

An bai wa Mugabe wa’adin sauka daga mulki ko a tsige shi

Shugaban kungiyar ‘yan mazan jiya, Chris Mutsvangwa, ya shaida wa BBC cewa, an riga an gama da Mr Mugabe a fagen siyasa domin babu wani tasiri da zai yi. Mai magana da yawun jam’iyyar kasar mai mulki ta Zanu-PF ya ce, yanzu Mr Mugabe ba shi da wani iko. Jam’iyyar wadda tuni ta cire shi […]

Nigeria: Hatsarin jirgin kasa ya kashe mutane a Lagos

A kalla mutum uku ne suka mutu bayan an yi hatsarin jirgin kasa a unguwar Agege da ke birnin Legas a kudancin Najeriya

Nigeria: Hatsarin jirgin kasa ya kashe mutane a Lagos

Shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar jiragen kasa ta Najeriya da ke da hedikwata a Legas, Yakubu Mahmud, ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a lokacin da wata motar tirela da take kokarin tsayawa ta daki jirgin kasan. Jirgin dai ya taso ne daga yankin Ijoko zai tafi yankin Ido da […]

Buhari Zai Kashe Naira Biliyan Daya a Tafiye-Tafiye a 2018

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana shirin kashe kimanin naira biliyan daya a badi wajen tafiye-tafiye, kamar yadda daftarin kasafin kudin kasar wanda ofishin kula da kasafin kudin kasar ya bayyana.

Buhari Zai Kashe Naira Biliyan Daya a Tafiye-Tafiye a 2018

Kamar yadda hukumar ta ce shugaban zai kashe naira miliyan 751.3 wajen tafiye-tafiyen kasashen ketare, yayin da zai kashe naira miliyan 250.02 wajen tafiye-tafiyen cikin gida. Haka zalika daftarin kasafin kudin ya bayyana cewa za a kashe naira miliyan 907 wajen sayen sabbin motoci da kuma sayo kayayyakin gyaransu a shekarar 2018. Har ila yau […]

Russia 2018: Italiya ta gamu da ‘babban bala’i’

Cikin kuka golan Italiya Gianluigi Buffon ya ba wa 'yan kasarsa hakuri, lokacin da ya yi ritaya daga taka leda, bayan sun gaza samun cancantar zuwa gasar Kofin Duniya.

Russia 2018: Italiya ta gamu da ‘babban bala’i’

Sweden ce ta rike wa Italiya wuya har suka tashi canjaras babu ci a birnin Milan, abin da ya hana wa kasar damar zuwa Rasha badi karon farko tun 1958. Karo hudu a tarihi Italiya tana lashe gasar Cin Kofin Duniya. Sakamakon dai na nufin kungiyar kwallon kafar Italiya ta Azzurri ba za ta halarci […]

Magani Mai Fasahar Dijital Zai Shigo Kasuwa

Hukumomin Amurka sun amince a fara sayar da wata kwayar magani ta fasahar dijital karon farko a duniya.

Magani Mai Fasahar Dijital Zai Shigo Kasuwa

Kamfanin Japan mai suna Otsuka ne ya samu izinin sayar da nau’in maganin da yake sarrafawa don masu larurar kwakwalwa da ake kira Abilify dauke da wani dan kankanin maballi a kowacce kwaya. Da zarar an hadiyi kwayar maganin, sai ta aika sako zuwa wani abu da za a manna wa jikin maras lafiya wanda […]

Zamu Fadawa Buhari Damuwarmu Idan Yazo – Igbo

Wasu al'ummar Igbo a yankin Kudu Maso Gabashin Najeriya sun yi maraba ga ziyarar da shugaban kasar zai kai jihohinsu daga ranar Talata.

Zamu Fadawa Buhari Damuwarmu Idan Yazo – Igbo

Akasarin mutanen da BBC ta zanta da su ta wayar tarho sun ce suna wa Shugaba Muhammadu Buhari maraba a wannan ziyara ta farko da zai kai yankin. Wasu Igbo dai sun sha sukar Muhammadu Buhari kan yadda suka ce ba ya damawa da al’ummar yankin a gwamnatinsa. Al’amarin da ya zafafa rajin ballewa daga […]

Nigeria: Wane bangare Buhari zai fi kashe wa kudi a kasafin 2018?

Najeriya ta bayyana kasafin kudinta na 2018, wanda gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke fatan zai samar da yanayin cigaba daga halin karayar tattalin arzikin da kasar take fama da shi.

Nigeria: Wane bangare Buhari zai fi kashe wa kudi a kasafin 2018?

Shugaba Buhari ya bayyana kasafin kudi na Naira tiriliyan 8.6 a gaban majalisar kasar, wanda ya ce zai samar da ayyukan yi ga matasa da kuma sabbin gine-gine a kasar. A bana ne Najeriya ta fita daga matsalolin koma-bayan tattalin arziki a hukumance bayan faduwar farashin man fetur, a shekarun baya. A jawabin da ya […]