Najeriya: ASUU Ta Janye Yajin Aiki

Najeriya: ASUU Ta Janye Yajin Aiki

Kungiyar malaman jami’o’i a Najeriya ta ASUU ta janye yajin aikin da take yi wanda ta kwashe sama da wata guda tana yi. Amma kungiyar ta janye yajin aikin ne da kashedin cewa za a biya masu bukatunsu nan da watan Oktoba mai zuwa a cewar jaridar Punch. Kafofin yadan labaran kasar da dama musamman […]

Hadiza Gabon ta soma fitowa a fina-finan Nollywood

Hadiza Gabon ta soma fitowa a fina-finan Nollywood

Jarumar ta shaida wa Nasidi Adamu Yahaya cewa ta fara gwada sa’arta a fina-finan Nollywood ne domin ta gwada basirar da take da ita ta yin fina-finai a bangarorin daban-daban. A cewarta, “Ba wannan ne karon farko da na soma yin fim da turanci ba. Lokacin da na je Amurka, na fito a fina-finan turanci, […]

Mayakan Saman Najeriya Sun Rugurguza Sabbin Sansanonin Boko Haram a Dajin Sambisa

Rarraba Dubi ra’ayoyi Jiragen leken asiri na sojojin yakin saman Najeriya sun gano wasu sabbin sansanoni da kungiyar Boko Haram ke ginawa a dajin Sambisa kuma sun rugurguzasu da lugudan wuta

Mayakan Saman Najeriya Sun Rugurguza Sabbin Sansanonin Boko Haram a Dajin Sambisa

Babban hafsan hafsoshin sojojin saman Najeriya Air Marshall Sadique Abubakar yace jiragen leken asirinsu sun gano yunkurin wasu mayakan Boko Haram na sake kafa sabbin sansanoni a dajin Sambisa. Sun gano wurare guda hudu da yan ta’addan ke akai, dalilin ma kenan da yasa suka kaddamar da shirin sintirin OPERATION RUWAN WUTA a wannan dajin. […]

Girgizar kasa ta hallaka sama da mutum 200 a Mexico

Wata mummunar girgizar kasa ta faru a tsakiyar birnin Mexico, inda ta hallaka mutane sama da 200, yayin da dama suka jikkata, wasu kuma ta rutsa su a cikin buraguzan gine-gine da suka rushe

Girgizar kasa ta hallaka sama da mutum 200 a Mexico

Girgizar wadda ta kai karfin lamba 7.1 a ma’aunin girgizar kasa, ta rushe gomman gine-gine, a babban birnin kasar, Mexico City, wadanda suka hada da wata makaranta, inda ake ganin ta rutsa yara a ciki. Tarin masu aikin sa-kai sun shiga taimaka wa masu aikin ceton gaggawa a kokarin da ake yi na gano masu […]

Kisan Musulmin Rohingya ya yi kama da kisan kiyashin Rwanda – Buhari

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya nemi Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta dauki mataki kan musgunawar da ake yi wa Musulmi 'yan kabilar Rohingya a kasar Myanmar.

Kisan Musulmin Rohingya ya yi kama da kisan kiyashin Rwanda – Buhari

A jawabin da ya gabatar a babban taron Majalisar Dinkin Duniya na 72, Shugaba Buhari, ya ce irin abun da yake faruwa a Myanmar ya yi kama da irin kisan kiyashin da ya aka yi Bosniya a shekarar 1995 da kuma Rwanda a shekarar 1994. Mutane a sassan duniya sun yi ta Allah-wadai kan irin […]

Nigeria: An tura jirgin yaki yankin Igbo

Rundunar sojin saman Najeriya ta shiga aikin dakile tashin hankali a kudu maso gabashin Najeriya mai suna 'Operation Python Dance II.

Nigeria: An tura jirgin yaki yankin Igbo

Wata sanarwar da darakatan hulda da jama’a na sojin saman Najeriya, Olatokunbo Adesanya, ya sanya wa hannu, ta ce kayayyakin aikin da sojin saman Najeriya ta tura wa jami’an aikinta na musamman a Fatakwal sun hada da jirgin yaki kirar Alpha Jet. Sanarwar ta kara da cewar an tura jirgin yankin ne domin a samar […]

Al-Bashir ya bukaci komawar wadanda suka tsere daga Darfur Daga Nura Ado Suleiman

Shugaban kasar Sudan, Omar Hassan al Bashir ya bukaci mazauna yankin Darfur da suka tsere daga gidajensu, su koma gida sakamakon kawo karshen yakin da aka gwabza wanda hallaka dubban mutane.

Al-Bashir ya bukaci komawar wadanda suka tsere daga Darfur Daga Nura Ado Suleiman

Akalla mutane sama da miliyan biyu da rabi ne suka tsere daga yankin na Darfur, sakamakon tashin hankalin da ya barke cikin shekara ta 2003, lokacin da ‘yan tawayen daga kananan kabilun yankin suka fara yakar sojojin kasar, bisa zargin kuntatawa yankin ta fannin siyasa da kuma tattalin arziki. Akasarin mutanen da suka tsere sun […]

‘Yar arewacin Nigeria ta ci gasar Komla Dumor ta BBC ta 2017

Wata 'yar jarida daga arewa maso gabashin Najeriya ce ta lashe lambar yabo ta BBC ta Komla Dumor ta bana.

‘Yar arewacin Nigeria ta ci gasar Komla Dumor ta BBC ta 2017

Amina Yuguda mai gabatar da labarai ce a gidan talbijin na Gotel da ke Yola, inda ta gabatar da labarai da dama har da wadanda suka shafi rikicin Boko Haram. Za ta fara aikin koyon sanin makamar aiki na tsawon wata uku a London cikin watan Satumba. An kirkiro lambar yabon ne don girmama Komla […]

Tasirin Sintirin Da Sojojin Najeriya Ke Yi a Sassan Kasar

A Najeriya sojojin kasar da dama na jibge a wasu yankuna domin gudanar da sintiri da atisaye, musamman domin kwantar da hankulan jama'a da kuma wanzar da zaman lafiya. Shin mene ne tasirin irin wannan sintiri?

Tasirin Sintirin Da Sojojin Najeriya Ke Yi a Sassan Kasar

 A sassa daban daban na Najeriya dakarun kasar kan gudanar da atisaye na musamman inda akan jibge su su yi kwana da kwanaki ko kuma su dauki wani tsawon lokaci suna atisayen. Akan kai dakarun ne yankunan da ke fama da wasu matsaloli na musamman, misali a yankin da ake fama da matsalar satar shanu […]

1 2 3 6